✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Najeriya mai shekaru 19 ta lashe Gasar Alkur’ani ta Duniya

Hajara Ibrahim Dan’azumi Gombe ta lashe gasar karatun Alkur'ani ta Duniya da mako 99.5

Wata ’yar Najeriya mai shekaru 19 mai suna Hajara Ibrahim Dan’azumi, ta lashe gasar karatun Alkur’ani ta Duniya ta bana.

Malama Hajara ta zama Gwarzuwar Shekara ce bayan da ta samu maki 99.5 a Gasar Hashimite ta Karatun Alkur’ani da Tajwidi ta Mata ta Duniya.

Hajara, wadda ta wakilci Najeriya, a gasar karatun Alkur’ani Izu 60 da Tajwidi, ta yi nasarar doke mahaddata Alkur’ani 40 daga kashe 38 da suka fafata a gasar.

Karo na 18 da aka gudanar da Gasar Karatun Alkur’ani ta Hashemite da gwamnatin kasar Jordan ta gudanar ta kuma karbi masaukin baki.

Malama Hajara dalibar aji biyu ce a Jami’ar Jihar Gombe da kuma  Makarantar Islamiyya ta Abubakar Siddiq Islamiyya da ke jihar.

Kafin yanzu, Malama Hajara Dan’azumi ce ta zo ta hudu a rukunin haddar Izu 40 a gasar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 34 da aka gudanar a Jihar Legas.

A waccan gasar ta samu maki 97.1 a yayin da kanwarta Maryam ta zo ta daya a rukunin Izu 10 da Tangimi; daya ‘yar uwarta Safiya kuma, ta zo ta 8 a rukunin Izu 40.

Mahaddata 41 daga kasashe 39 ne dai suka fafata a gasar da aka gudanar a kasar Jordan, wadda Hajara ta lashe.

Gwamnan jihar Gombe ya bayyana farin cikinsa tare da alfahari da wannan nasara da matashiyar ta samu a fannin Alkur’ani a duniya.

Ya bayyana jinjinarsa ga malamanta da kuma iyayenta bisa jajircewarsu da ta kai matashiyar ga wannan mataki na daukaka.

Ya bayyana cewa hakan zai ba da  kwarin gwiwa musamman ga matsa mata su jajirce wajen neman ilimi domin samun ingantacciyar rayuwa.