✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Sheikh Dahiru Bauchi ta zama mai ba Gwamnan Gombe Shawara

Amina Sheikh Dahiru Bauchi ta ba gwamnan Gombe shawara ta musamman kan Harkokin Almajirai da Karatun Tsangaya

’Yar Sheikh Dahiru Bauchi, Amina ta zama Mai ba da Shawara ta Musamman kan Harkokin Almajirai da Karatun Tsangaya ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.

Sanarwar da sakataren gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya fitar ta ce gwamnan ya ya nada Hajiya Amina Dahiru Bauchi ne tare da wasa wasu mutum bakwai saboda rawar da za su taka wajen ciyar da jihar gaba a bangarori daban-daban.

Sanarwar mai dauke da Sanya hannun Babban Daraktan Yada Labarai na gidan gwamnatin Jihar Isma’ila Uba Misilli, ta ce sauran sabbin mashawartan gwamnan na musamman sun hada da AIG Zubairu Mu’azu Mai Ritaya a matsayin mai ba da shawara kan harkar tsaro.

Aishatu Adamu ita ce mashawarciya kan harkar zuba jari da shirya-shirye na musamman; sai Madam Finney David, a bangaren harkokin ta.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai Ritaya ACP Ibrahim Bappah a shi ne Babban Daraktan hukumar tsaron da gwamnatin jihar ta kirkiro na cikin (GOSTEC).

Ibrahim Saidu Umar, ya zama Babban Mai Taimaka wa Gwamna na 1 kan harkokin tsare-tsare, sai Yakubu Sarma, a bangaren ayyukan gamagari.