✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar shekara 8 ta rubuta wa Buhari wasika

Wata yarinya ’yar shekara takwas da haihuwa ta rubuta wasika ga Shugaba Muhammadu Buhari tana tambayar yadda za ta yi ta bayar da gudunmawar kudin…

Wata yarinya ’yar shekara takwas da haihuwa ta rubuta wasika ga Shugaba Muhammadu Buhari tana tambayar yadda za ta yi ta bayar da gudunmawar kudin da ta tara don a yaki annobar coronavirus.

Yarinyar daga jihar Delta ta ce a halin yanzu Najeriya na matukar bukatar kudin a fafutukar da take yi don dakile yaduwar annobar.

Kamar yadda ta rubuta a wasikar tata, Vera Akpan ta ce “Ina da asusu wanda a ciki yanzu haka nake da N2,350 da na so na bayar ga wani gidan marayu da ke Warri.

“Amma bukatar da kasa ke ciki na da matukar muhimmanci a gare ni. Kudin ba su da yawa amma, a matsayina na yarinya, ga su nan a karba da hakuri”.

Vera dai daliba ce da ke takaicin yadda annobar ta coronavirus ta tilasta rufe makarantar da take zuwa.

“Rufe makarantu saboda annobar coronavirus ya kawo tsaiko a karatunmu, amma yin hakan alheri ne”, inji ta.

’Yan Najeriya da dama dai a daidaikunsu ko a kungiyance sun bayar da gudnmawar kudi don yakar annobar ta COVID-19, lamarin da ya sa Vera ma ta ga ya kamata ta nuna kishin kasa.

Wasu daga cikin mutanen da suka bayar da gudunmawar dai su ne Aliko Dangote, da Tony Elumelu, da Femi Otedola, da Abdulsamad Rabiu, da Herbert Wigwe, da Segun Agbaje, da Atiku Abubakar, da kuma Tuface Idibia.

Kadan daga cikin kamfanonin da suka bayar kuwa sun hada Access Bank, da Zenith Bank, da Guaranty Trust Bank da bankin UBA, da kuma Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC.