✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yara 10 sun kone kurmus a gobarar makaranta

Akalla yara kanana 10 ne suka kone kurmus a gobarar da ta tashi a dakin kwanan daliban wata makarantar firamare da ke Arewa maso Yammacin…

Akalla yara kanana 10 ne suka kone kurmus a gobarar da ta tashi a dakin kwanan daliban wata makarantar firamare da ke Arewa maso Yammacin kasar Tanzaniya.

Wani jami’i da ya bayyana faruwar lamarin ya ce wasu yara bakwai kuma sun samu kuna a sassa daban-daban na jikinsu.

“Yara 10 sun kone kurmus har ba a iya game su, sai uku cikin bakwan da suka samu kuna a sassa daban-daban na jikinsu da ke cikin mawuyacin hali”, inji Kwamishinan Yankin Kagera, Marco Gaguti.

Ya ce gobarar ta tashi ne ranar Lahadi da misalin karfe 11 na dare a dakin kwanan dalibai mai dauke da kananan yara maza 74 a makarantar maza zalla da ke kauyen Itera na Karamar Hukumar Kyerwa.

“’Yan sanda da ’yan kwana-kwana da makwabtan makarantar sun ceci mafi wayan yaran da gobarar ta rutsa da su”, inji Gaguti da ke wurin da gobarar ta auku.

Ya ce ba su san abin da ya haddasa gobarar ba amma ya kafa da kwamitin bincike da ya kunshi ’yan sanda da kamfanin wutar lantarki da jami’an tsaro na fararen kaya.

“Muna kyautata tsammanin wadannan mutanen za su gano musabbabin gobarar”, inji shi.

Ya kara da cewar an rufe makarantar na kwanaki bakwai domin a samu damar gudanar da cikakken bincike.