Yarinya ’yar fim ta gina wa mahaifiyarta gida | Aminiya

Yarinya ’yar fim ta gina wa mahaifiyarta gida

    Abbas Dalibi

Shahararriyar  ’yar barkwancin nan a masana’antar fim ta Nollywood Emmanuella Samuel mai shekara 10, ta gina wa mahaifiyarta gida na alfarma.

Emmnuella ta sanar da hakan ne a shafinta na Instagram inda ta wallafa wasu hotunanta tare da mahaifiyarta da kuma wasu ’yan uwanta a cikin sabon gidan.

“Na gina wannan gida sabo don ke mahaifiyata, saboda kwarin gwiwa da kike ba ni da addu’arki a gare ni da taimakon da kike yi min.

“Ko da yake na san burinki matsakaicin gida ne, to gashi nan, amma ki kwana da sanin zan kammala gina miki katafaren gida cikin shekara mai zuwa.

“Ki gafarce ni, yin hakan ne zai sa ba za mu shiga wuta a lahira ba” inji ta.

Wannan mataki na shaharariyar ’yar wasan barkwanci mai shekaru 10 kacal ya dauki hankalin mabiyanta ta kafar Instagram su kimanin dubu 471, inda labarin ya karade kafafan sadarwa na zamani.

Aminiya ta kawo maku hotunan gidan da Emanuella ta gina wa mahaifiyar tata.

Shahararriyar ’yar wasan barkwanci a masana’antar fim ta Nollywood Emmanuella Samuel ta gina wa mahaifiyarta gida.