✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaro ya haifi dan uwan tagwaicinsa

Wata jaridar kasar Sin a ruwaito yadda wani yaro dan shekara biyu ya haifi dan uwan tagwaicinsa, bayan an yi masa aikin fida, inda likitoci…

Wata jaridar kasar Sin a ruwaito yadda wani yaro dan shekara biyu ya haifi dan uwan tagwaicinsa, bayan an yi masa aikin fida, inda likitoci suka gano yadda jariri ya yi ta girma a cikin yaron.
diao Feng, yaron da ya fito daga yankin Huadi a kasar China ya samu kansa a gadona asibiti ne bayan da aka ga cikinsa yana ta girma, kuma yana fama da matsalar shakar numfashi, don haka aka dauki hoton cikinsa, inda aka gano Feng na dauke da dan tayin tagwaicinsa.
dan tayin ya yi tsawon sentimita 20, kuma kasusuwan jikinsa sun fara bunkasa, wadanda suka hada da yatsu da tafukan kafa. Sun yi girman da suka mamaye kashi biyu bisa uku (2/3) na fadin cikin yaron, kamar yadda likitoci suka bayyana.
Irin wannan al’amari na manannanun ’yan biyu, wanda a Kimiyyar likitanci ake yi wa lakabi da cryptodidymus, ya kai makura, ta yadda za a iya cewa ba a taba ganin aukuwarsa a fannin likitanci ba, kamar yadda Inkuisitr ta ruwaito. Manannun ’yan biyu na aukuwa ne da zarar kwayayen haihuwa sun ki rabuwa.