✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashawa: Yau Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje

Lauyoyi sun zauna, ana jiran isowar alkali a ci gaban shari'ar zargin Ganduje da cin hanci da almundahana a zamanin mulkinsa a mastayin gwamnan Kano.

A yau ne za a ci gaba da sauraron shari’ar zargin Shugaban Jam’iar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ake zargi da cin hanci da almundahana a zamanin mulkinsa a mastayin gwamnan Kano.

Wakilin Aminiya a kotun ya ruwaito cewa lauyoyin bangarorin sun zauna, ana jiran isowar alkalin kotun.

Za a ci gaba da zaman ne bayan gaza gurfanar da Ganduje da sauran wadanda ake zargi a lokacin zaman farko ranar 17 ga wata, a shari’ar da hukumar yaki da almundahana ta jihar Kano ta shari’ar da shigar kara.

Hukumar na zargin Ganduje da mai dakinsa da dansa da wasu makusantansa da laifuka takwas da suka danganci rashawa da karkatar da dukiyar al’umma.

ِShugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado, ya zargi gwamnatin Ganduje, da karkatar da kudaden kananan hukumomi Naira biliyan 51.3.

A cewarsa, hukumar ta bankado yadda tsohuwar gwamnatin ta ciri Naira miliyan 600 daga asusun gwamnatin Kano zuwa wani kamfani da Ganduje yake darakta kuma mai dakinsa ce ke gudanar da asusunsa.

Muhuyi ya ce za su gabatar da shaidu da hujjoji 15 kan zargin da ake wa tsohon gwamnan a gaban a gaban Babbar Kotun Jihar Kano.

Sai dai rashin bayar da sammaci ga Ganduje da matarsa da dansa da wasu mutane biyar ya kawo tsaiko ga gurfanar da su a ranar 17 ga wata.

Masu gabatar da kara lauyoyin gwamnati sun bayyana cewa ba su sami damar bayar da sammaci ga wadanda ake kara ba saboda wasu daillai.

Sun yi kokarin kotun ta ba su damar bayar da sammaci ga wadanda ake kara ta wasu hanyoyin daban.

Sai dai Barista Nuraini Jimoh wanda shi ne lauyan kariya ga wanda ake kara na shida Kamfanin Lamash ya soki rokon masu, inda ya kafa hujja da cewa a shari’a ta laifi ba a bayar da sammaci ta yin amfani da wasu kafofin sai dai hannu da hannu.

Alkalin kotun Mai sharia Usman Na’abba ya bayar da a sake mika wa wadanda ake kara sammaci sannan kotun ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu, 2024.