✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawan Hadiman da Gwamnan Kano ya nada yanzu sun kai 81

Gwamnan ya sake nada sabbin mukamai 42 a ranar Litinin.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada sabbin Hadimai 52 domin cike gurbin masu ba da shawara na musamman da manyan mataimaka na musamman a gwamnatinsa. 

Ya zuwa yanzu, gwamnan ya nada adadin mataimaka guda 81 ke nan.

Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da yammacin Litinin, inda ya ce sabbin nade-naden Hadiman 42 na daga cikin “kokarin Gwamnan na jan matasa a jiki”.

Wadanda da aka bai wa sabbin makaman sun hada da: bangaren Fasahar Sadarwa, Wayar da Kai, Watsa Labarai, Kula da Ayyuka, Ci gaban Kasuwanci da Tashoshin Mota.

Sauran bangarorin sun hada da; Kasuwanni, Fitilar Titin, Mawaka (Mawallafa), Al’amuran Kannywood, Kasuwar Waya, Makarantun Islamiyya, Tsaro, Harkokin Soja, Al’amuran Kasuwar Man Fetur, Karkara, Rediyo, Harkokin Ƙasashen waje, Ilimin Yara Mata, Ayyuka na Musamman I, Ayyuka na Musamman II da sauransu.

Bature ya ce, “Nade-naden za su fara aiki ne nan take, inda ya ce ana sa ran duk wadanda aka nada za su sauke nauyin da aka dora musu.

A wata sanarwa da ya bayyana nadin mukamai na musamman guda 10, Bature ya ce nadin ya zama wani fage na cika alkawuran da ya yi lokacin yakin neman zabe.

Sabbin masu ba da shawara da aka nada su ne; Garba Dirbunde, Wakili Aliyu Garko, Air Commodore Yusha’u Salisu Tudunwada Wada, Musa Ado Tsamiya, da Gwani Musa Falaki.

Sauran su ne; Dokta Sulaiman Wali Sani, Farfesa Auwalu Arzai, Ahmad Sawaba,, Tajuddeen Gambo da Baba Abubakar Umar.

Ya kara da cewa, “An yi nade-naden ne bisa cancanta, aminci da kuma jajircewa wajen yi wa al’ummar jihar Kano hidima”.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 16 ga watan Yuni ne gwamnan ya sanar da nadin mataimaka 14, yayin da kuma a ranar 18 ga watan Yuli gwamnan ya sake nada mutum 15 a matsayin masu ba da shawara na musamman.