✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yerima ya zama sabon kakakin Rundunar Soji Kasa ta Najeriya

Birgediya Mohammed Yerima ya maye gurbin Sagir Musa

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta nada Birgediya Mohammed Yerima a matsayin sabon mai magana da yawunta.

Sashen Hulda da Jama’a na Rundunar, ya sanar a Talata cewa Birgediya Yerima ya shi ne ya maye gurbin Birgediya Sagir Musa wanda aka sauya wa wurin aiki

Sanartwar ta ce kafin sabon nadin, Birgediya Yerima shi ne Mataimakin Daraktan mai kula da Adana a Hedikwatar Tsaro. Ya kuma taba zama Daraktan Sashenta na Hulda da Jama’a.

Aminiya ta gano cewa hakan na daga cikin sabbin sauye-sauyen da sabon Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Manjo-Janar Ibrahim Attahiru ya fara yi.

Majiyarmu ta tsaro ta ce, sauye-sauyen a Sashen Hulda da Jama’a da a baya Birgediya ke rikon kwarya na da matukar Muhimmanci.

Sagir Musa ya ci gaba da yin rikon kwaryar ne tun bayan da aka sauya wa tsohon kakakin Rundunar, Birgediya Sani Kukasheka Usman wurin aiki.