✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a dawo wa da Najeriya £4.2m da James Ibori ya boye a Birtaniya

Za a yi amfani da kudaden da aka kwato a wasu manyan ayyuka, ciki har da titin Abuja zuwa Kano.

Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu a kan wata yarjejeniya da Gwamnatin Birtaniya domin a dawo mata da Yuro miliyan hudu da dubu dari biyu da tsohon Gwamnan jihar Delta, James Ibori ya boye a can.

Da take jawabi yayin rattaba hannu a kan dokar, Jakadiyar Birtaniya a Najeriya, Misis Catriona Laing ta ce daga karshe dai a yanzu za a dawo wa da Najeriya kudaden bayan shafe tsawon shekaru ana tafka shari’a a kansu.

A shekarar 2016 ne dai Najeriya ta rattaba hannu da Gwamnatin ta Birtaniya a kan dawo mata da kudaden da aka kwato daga iyalai da kuma makusantan tsohon Gwamnan a can.

Kazalika, a shekarar 2012, James Ibori ya amsa laifi a tuhume-tuhumen da ake yi masa a wata kotu a Birtaniya.

Tuhume-tuhumen dai na da ke da alaka ne da zambar kudade, hadin baki da kuma damfara.

Daga bisani dai kotun ta yanke masa zaman gidan yari na shekaru 13.

Yayin bikin sanya hannun dai, Ministan Shari’a Kuma Babban Luyan Gwamnati, Abubakar Malami ya ce za a yi amfani da kudaden da aka kwato ne wajen kammala ayyukan Gadar Neja ta Biyu da kuma ayyukan titunan Abuja zuwa Kano da na Legas zuwa Ibadan.