✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara korar masu fallasa sirrin gwamnati daga aiki

Gwamnatin ta ce hakan ya saba da dokokin aikin gwamnati.

Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar fara korar duk jami’in da ta samu da hannu a fallasa takardun sirrin gwamnati ta kafafen sada zumunta na zamani.

Shugabar Ma’aikata ta Kasa, Dokta Folasade Yemi-Esan ce ta yi gargadin a wata wasika da ta fitar mai dauke da kwanan watan biyu ga Agustan 2021.

Wasikar, mai taken ‘Fallasa sirrin gwamnati ta kafafen sada zumunta ba bisa ka’ida ba’ na dauke da lambar HCSF/3065/Vol.1 /94.

Karo na biyu kenan da gwamnatin ke bayar da irin wannan gargadin a cikin shekara daya.

A cewar wasikar, “Wannan ba dabi’ar da za mu lamunta ba ce ta fallasa wasikun gwamnati, kwafin dokoki, takardun taruka ko kowanne irin sirri na gwamnati ta kafafen sada zumunta.

“Hakan ba karamin sakaci ba ne da kuma saba wa rantsuwar da ma’aikata suka yi lokacin daukarsu aiki, wanda kuma zai iya kai wa ga kora daga aiki, kamar yadda dokokin aikin gwamnati suka tanada.

“Saboda haka, Manyan Sakatarori da shugabannin hukumomi su yi kokarin yada wannan wasika ga dukkan ma’aikata don su san da ita,” inji sanarwar.

Ko a watan Maris sai da gwamnatin ta fitar da makamanciyar irin wannan sanarwar tare da barazanar daukar kwakkwaran mataki kan duk wanda ya yi kunnen uwar shegu da ita.