✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a halasta wa jami’an diflomasiyya sayen barasa a Saudiyya 

Mohammed bin Salman ya ɗaura ɗamarar kawo sauye-sauye da za su dace da sharholiya irin ta wannan zamani.

Saudiyya ta soma shirye-shiryen halasta wa jami’an diflomasiyya wadanda ba musulmai ba sayen barasa a kasar.

Wasu majiyoyi biyu da ke da masaniya kan shirin ne suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP) hakan a wannan Larabar.

“A yanzu za a halasta sayar da barasa ga jami’an diflomasiyya wadanda ba musulmi ba” wadanda a baya sai dai su shigo da ita kasar a cikin ’yar jakar diflomasiyya, in ji daya daga cikin majiyoyin.

Tun a shekarar 1952 ne dai aka haramta duk wani ta’ammali da barasa a Saudiyya.

Sanya haramcin a wancan lokacin na zuwa ne bayan da ɗaya daga cikin ’ya’yan Sarki Abdulaziz ya yi mankas da barasa, kuma a fusace ya harbe wani jami’in diflomasiyyar Birtaniya.

A shekarun baya-bayan nan dai an yi ta jita-jitar cewa za a halasta barasa a Masarautar da ke yankin Gulf, yayin da Yarima mai jiran gadon Masarautar Saudiyya, Mohammed bin Salman ya ɗaura ɗamarar kawo sauye-sauye — ciki har da buɗe silima da kade-kade da raraye-raraye cakude da maza — da za su dace da sharholiya irin ta wannan zamani.

Wata sanarwa da Gwamnatin Saudiyya ta fitar a wannan Larabar, ta ce mahukunta za su bijiro da sabbin tsare-tsare domin dakile kwararowar miyagun ƙwayoyi da barasa da sauran dangogin kayan maye da ake samu a hannun jami’an diflomasiyya ba bisa ka’ida ba.

A karkashin dokokin Saudiyya dai, shan barasa ko duk wani na ta’ammali da ita na iya janyo hukuncin cin tara, zaman gidan wakafi, bulala a bainar jama’a ko kuma korar mutum daga kasar idan ya kasance bako