✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kashe N805.7m don inganta tsaro a Hedikwatar EFCC

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da Naira miliyan 805.7 domin sayen kayayyakin inganta tsaro a Hedikwatar Hukumar EFCC da ke Abuja. Ministan Yada Labarai…

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da Naira miliyan 805.7 domin sayen kayayyakin inganta tsaro a Hedikwatar Hukumar EFCC da ke Abuja.

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana haka a Fadar Shugaban Kasa bayan taron Majalisar wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta a ranar Laraba.

“Daga 2011 zuwa shekarun da suka biyo, an kai hare-hare daban-daban a kan cibiyoyin Gwamnatin Tarayya da ginin Majalisar Dinkin Duniya da sauransu.

“Sakamakon wadancan hare-hare a 2011 da 2014 da  2018, Gwamnati Kwamitin Tantance Raunin Juna domin ganin yadda za mu kara kare ma’aikatu da sassa da ma hukumomin gwamnati.

“Lura da hakan, a yau EFCC ta gabatar wa Majalisar Zartarwar takardar neman amincewarta don sayan na’urorin zamani da za a girke a Helkwatar Hukumar.

“Akwai shingen bankado miyagu mai tsawon mita 900, da kayan aikin binciken mutane, da na’urorin binciken karafa guda hudu, da na’urorin binciken karfe na hannu guda biyu, da na’urar binciken jakunkuna da na’urar binciken abubuwa masu fashewa na hannu guda uku.

“Duk a kan miliyan N805.7 wanda ya kunshi kashi 7.5 na harajin VAT inda aka tsara kamala aikin a mako 12,” inji Ministan.