✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rataye malamin addini kan fashi a banki

Kowannensu ya amsa irin rawar da ya taka a fashin bankunan

An yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani malamin addini, Adewale Adelu da wasu mutane biyar bisa samun su da laifin fashi da makami a bankuna a Jihar Ondo.

Babbar kotun jihar ta samu Adawale da abokansa da laifin kai hari tare da yin fashi a wasu bankunan kasuwanci a Akure, babban birnin jihar da kuma garin Idanre.

Sun yi fashin ne shekaru 13 da suka gabata a reshen bankin Diamond (Access a yanz) da ke Akure da kuma reshen First Bank da ke Idanre, hedikwatar Karamar Hukumar Idanre.

Mai shari’a Yemi Fasanmi wanda ya jagoranci shari’ar ya yanke musu hukuncin ne bayan sun amsa cewa sun aikata laifin da ake tuhumar su.

A ranar 14 ga Yuli, 2022 aka fara gurfanar da su kan zargin hada baki, fashi da makami, da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba. 

Bayan gurfanar da su a gaban kotu, alkali ya bayar da umarnin tsare su a gidan yarin Olokuta da ke jihar.

A yayin shari’ar, lauya mai gabadatar da kara, Salami, ya gabatar da shaidun da ke nuna cewa wadanda aka yanke wa hukuncin, sun yi amfani da nakiyoyi da kuma bindigogi kirar AK-47 wajen yin fashin a rasssan bankunan, lamarin da ya girgiza al’ummar Akure da Idanre. 

Bayan kowannensu ya amsa irin rawar da ya taka a fashin bankunan, Mai Shari’a Fasanmi, ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan kowanne daga cikin laifukan.