✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a saka nakasassu 40,000 a cikin ’yan N-Power

nan ba da jimawa ba kuma za a bayar da tallafin karatu ga dalibai masu bukata ta musamman.

Hukumar da ke Kula da Masu Bukata ta Musamman ta Kasa ta ce akalla masu bukatar 40,000 ne aka dauki bayanansu domin su shiga ciki wadanda za su amfana da rukuni na ‘C’ na shirin N-Power.

Babban Sakataren hukumar, James Lalu ya lura cewa saka su a cikin shirin wani yunkuri ne na kara basu dama kamar sauran mutane.

Mista Lalu, yayin wani taron ’yan jarida ranar Alhamis domin bayyana nasarorin hukumarsa a cikin shekara daya da kafa ta, ya ce suna aiki ba dare ba rana wajen sauya tunanin masu bukatar ta musamman don ganin an daina daukarsu a matsayin wani nauyi a al’umma.

Ya kuma yaba wa gwamnati mai ci wajen yadda take kula da masu bukatar la’akari da yadda aka yi watsi da su a baya, tun bayan dawo wa mulkin dimokradiyya a Najeriya.

Shugaban ya kuma ce nan ba da jimawa ba za a bayar da tallafin karatu ga dalibai masu bukata ta musamman.

Mista Lalu ce har yanzu hukumarsa ba ta fara gurfanar da wadanda suka ci zarafin masu bukata ta musamman ba ne saboda suna ta kokarin wayar da kan mutane a kan dokar da ta hana yin haka ta 2018.