✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

za a samu mamakon ruwan sama da ambaliya ranakun Talata da Laraba a Pakistan – NDMA

Hukumar Kula da Yanayi ta kasar Pakistan ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a Kudancin lardin Sindh ranar Talata da Laraba, da zai haddasa…

Hukumar Kula da Yanayi ta kasar Pakistan ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a Kudancin lardin Sindh ranar Talata da Laraba, da zai haddasa ambaliya.

A hasashen yanayin ya ce akwai yiwuwar samun ambaliya ranar Talata a Kudu maso Yammacin lardin Balochistan, sakamakon toshewar magudanan ruwa.

Haka zalika ita ma hukumar kula da aukuwar bal’o’i ta kasar (NDMA), ta yi makamancin hasashen a Kudancin Balochistan din na tsawon kwana biyar.

Haka kuma ta ce akwai yiwuwar samun wata ambaliyar sakamakon tumbatsar Rafin Kabul da Indus a wadannan kwanakin.

Don haka jukumar ta shawarci masu ruwa da tsaki da su yi kyakkyawan shirin tunkarar lamarin, domin rage asarar rayuka da dukiya da za a iya samu.

Haka kuma ta shawarci makiyaya da su kau da dabbobinsu daga yankunan da ke kusa da Rafin zuwa tsaunuka, don gudun asara.

Daga faduwar damina a ranar 14 ga watan Yuni a kasar dai zuwa yanzu, ambaliya ta yi sandiyar mutuwar mutum 820 da jikkatar 1,315 a lokuta daban-daban.