✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a shafe kwana 3 ana ruwan sama da tsawa a Jihohin Arewa

Za a shafe kwana 3 ana ruwan sama da tsawa a Jihohin Arewa

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta ce akwai yiwuwar a sami hadari da ruwan sama hadi da tsawa daga ranakun Litinin zuwa Laraba a fadin kasar.

Hasashen, wanda hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ya kuma ce za a sami hadari da ruwa a wasu sassan Jihohin Arewacin Najeriya, da kuma yiwuwar samun tsawa a wasu sassan Adamawa da Kaduna da Taraba.

NiMet ta ce za a sami tsawa a Jihohin Sakkwato da Zamfara da Borno da Taraba da Adamawa da Kaduna da Kano da Katsina da Bauchi da Jigawa da Gombe da kuma Kebbi, zuwa yammaci.

Ta kuma ce, “Za a fuskanci hadari da ranar jifa-jifa a wasu sassan Arewa ta Tsakiya, da yuwuwar samun tsawa a wasu sassan Abuja da Filato da Binuwai da Nasarawa.

“Daga bisani kuma za a samu tsawa a ilahirin yankin. Kazalika, za a fuskanci hadari da ruwa a jihohin Kudancin Najeriya da kuma yuwuwar samun tsawa a Jihohin Legas da Kuros Riba da Akwa Ibom da Ribas da Delta da kuma Bayelsa,” in ji hukumar.

NiMet har ila yau ta ce za a samu zafin rana da hadari jifa-jifa a fadin Arewa Najeriya da yiwuwar samun ruwan sama hade da tsawa da safe a sassan Sakkwato da Kebbi da Taraba da kuma Adamawa.