✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi wa ’yan mata miliyan 7 rigakafin cutar kansar mahaifa a Najeriya

"Wannan shi ne shirin irinsa mafi girma a nahiyar Afirka"

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) za su yi wa ‘yan mata miliyan 7.7 rigakafin cutar kansar mahaifa a Najeriya.

Wannan shirin dai shi ne irinsa mafi girma nahiyar Afirka, in ji Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Muhammad Ali Pate.

Ministan, wanda ya bayyana hakan yayin kaddamar da rigakafin a Abuja, inda kuma ya bayyana matukar damuwarsa kan cutar a kasar nan, yana mai cewa, “Asarar mata kusan 8,000 a duk shekara daga cutar da ake iya rigakafinta ba abu ne da za a amince da shi ba.”

Pate ya kuma ce da wannan kaddamarwar, yanzu ke nan Najeriya ta shigar da allurar rigakafin cutar a cikin tsarin rigakafinta na yau da kullum a hukumance.

Pate ya jaddada cewa ceton rayuka da tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya su ne jigon kudirin inganta lafiyar al’umma na Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya kuma bayyana cewa, “A matsayina na uba, ni kaina, ina da ‘ya’ya mata hudu, dukkansu sun yi allurar rigakafin cutar kansar mahaifa guda daya don kare su daga cutar.

“Ina so in yi kira ga ‘yan uwanmu iyaye da su tabbatar da cewa ‘yan matanmu sun karbi allurar rigakafin kamuwa da cutar kansar mahaifa”.

‘Yan mata masu shekaru 9 zuwa 14 za su sami kashi ɗaya na maganin rigakafin na HPV, wanda yake da tasiri wajen hana kamuwa da cutar.

Cutar kansar mahaifa dai ita ce ta biyu da take sanadin mutuwar mata masu shekaru 15 zuwa 44.

Wakilin WHO a Najeriya, Dokta Walter Kazadi Mulombo, ya ce wannan wani muhimmin lokaci ne a kokarin da Najeriya ke yi na rage yawaitar yaduwar cutar, wacce ya ce za a iya kawar da ita ta hanyar rigakafi.

“Mun himmatu wajen tallafa wa gwamnati ta kara samun damar yin amfani da allurar rigakafin cutar ta don kare lafiya da jin dadin rayuwar mata a nan da wasu shekaru masu zuwa,” in ji jami’in na WHO.

Ita ma a nata bangaren, UNICEF ta taka muhimmiyar rawa a shirin, inda ta siyo rigakafin cutar kusan miliyan 15 a madadin Gwamnatin Najeriya.

Taron kaddamar da shirin rigakafin na tsawon kwanaki biyar, ya kunshi makarantu da al’umma a fadin jihohi 16 da kuma Abuja.

A haka kuma, maganin zai zama wani ɓangare na tsarin rigakafi na yau da kullum a cibiyoyin kiwon lafiya.
Ana sa rai Kashi na biyu zai fara aiki a watan Mayun 2024, wanda zai ƙunshi jihohi 21.