✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu daukaka kara kan hukuncin kotu —Sadiq Wali 

Wali ya ce lauyoyinsa na nazarin hukuncin kotun kafin ya daukaka kara.

Dan tarakar gwamnan Kano a Jam’iyyar PDP da kotu ta soke, Sadiq Aminu Wali ta ayyana Mohammed Abacha, ya ce zai daukaka kara.

A ranar Alhamis wata kotun tarayya da ke jihar ta yanke hukuncin ayyana Mohammed Abacha a matsayin halastaccen dan takarar jam’iyyar.

Sadiq Wali ya ce, “Ni ba lauya ba ne, amma na san wannan shari’ar cike take da kurakurai. Lauyoyina za su nazarin hukuncin.

“Kotun farko ta ce duk wani shugabancin jam’iyyar da ya gudanar da zabe ba bisa tsarin shugabancin jam’iyya na kasa ba, zaben bai halasta ba.

“Ina tunanin akwai kuskure babba a hukuncin kotu, don haka za mu garzaya gaba don kwatar ’yan PDP,” in ji Wali.

Alkalin da ya yanke hukuncin, A.M Liman, ya umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta sauya sunan Wali da Mohammed Abacha.

Kotun dai ta amince da zaben fid-da gwani da tsagin shugabancin jam’iyyar karakshin, Shehu Wada Sagagi ya gudanar, wanda Mohammed Abacha damar lashe.

Da yake bayyana rashin jin dadinsa kan hukuncin kotu, Wali wanda da ne ga tsohon ministan harkokin kashen waje, Aminu Wali, ya ce zai tafi kotun daukaka kara.

Sai dai wannan hukunci ba zai yi wa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar dadi ba, duba da yadda yake sa ran samun miliyoyin kuri’a a jihar.

Dalili kuwa shi ne, ana zargin tsagin shugabancin jam’iyyar na Shehu Wada Sagagi yana yi wa tsohon uban gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso aiki ta karkashin kasa ne.

Idan ba a manta ba tsagin na Sagagi ya goyi bayan neman takarar shugaban kasa na Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike a lokacin zaben fid-da-gwani.

Sadiq Wali, ya nemi magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu kan hukuncin da kotun ta zartar, inda ya ce lauyoyinsa na nazarin hukuncin kafin zuwa kotun daukaka kara.