✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu sa kafar wando daya da gwamnati in aka janye tallafin mai – NLC

NLC ta yi barazanar shirya gagarumar zanga-zanga, muddin gwamnati ta cire tallafin.

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) reshen Jihar Gombe ta yi barazanar sanya kafar wando daya da Gwamnatin Tarayya kan muddin ta kuskura ta janye tallafin man fetur.

Kungiyar ta kuma ce tana kokarin hada kan ’ya’yan ta da ma na wasu kungiyoyin fararen hula don gudanar da zanga-zangar lumana a ranar 27 ga watan Janairu, matukar gwamnatin ta janye tallafin man.

Shugaban kungiyar a Jihar Gombe, Kwamared Adamu Musa Kenny, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a sakatariyar kungiyar ranar Juma’a, jim kadan bayan fitowarsu daga zaman da kungiyar tayi kan lamarin.

NLC dai ta yi gargadin cewa cire tallafin man zai kara jefa kasar nan cikin rudani, la’akari da yadda yanzu haka ma ake fama da kuncin rayuwa na matsin tattalin arziki ga hauhawar farashi a kodayaushe.

Kwamared Adamu, ya kuma ce kungiyar za tayi dukkan mai yiwuwa don tabbatar da cewa Gwamnatin ta dakatar da aniyarta ta cire tallafin.

A cewarsa, NLC ta kammala hada kan mambobinta na da na fararen hula da su fito a ranar ta 27, domin gudanar da babbar zanga-zangar a Abuja, karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa.

Shugaban ya ce tuni suka riga suka sanar da jami’an tsaro don basu kariya a lokacin zanga-zangar, wacce ya ce za ta kasance ta lumana.

Kungiyar dai ta ce cire tallafin man zai janyo karin farashinsa a gidajen sayar da shi, su kuma ba za su zuba ido suna ganin haka ta faru ba.