✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu taimaka wa Najeriya ta gyara matatun manta – Saudiyya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta yi alkawarin zuba jari domin farfaɗo da matatun man Najeriya da kuma taimaka wa gwamnati ta aiwatar da tsare-tsaren daidaita darajar…

Gwamnatin kasar Saudiyya ta yi alkawarin zuba jari domin farfaɗo da matatun man Najeriya da kuma taimaka wa gwamnati ta aiwatar da tsare-tsaren daidaita darajar Naira.

Yariman Saudiyya, Muhammad Bin Salman ne ya yi alkawarin yayin tattauna da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a gefen taron kasar da kasashen Afirka da yake gudana a Riyadh, babban birnin kasar.

Saudiyya ta kuma yi alkawarin tallafa wa Najeriya, ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN), domin a farfaɗo da darajar Naira.

Yarima Muhammad, a cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya kuma yabawa manufofin tattalin arzikin da Shugaba Tinubu yake aiwatarwa.

A cewar Yariman na Saudiyya, ƙasar shi ta ƙagu ta ga Najeriya tana bunkasa a karkashin Shugaba Tinubu, musamman a matsayinta na jagaba a Afirka.