✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: Hukunce-hukunce kotun daukaka kara da suka fi tayar da kura

Ana zargin tufka da warwara a wasu hukunce-hukunce da Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta yanke kan wasu shari'o'in zaben 2023 masu kama da juna…

Wasu hukunce-hukunce da Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta yanke a baya-bayan nan sun kawo zargin tufka da warwara a hukuncin da alkalanta ke yankewa a shari’o’in zabe.

Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ita ce mai biye da Kotun Koli, kuma ita ke da hurumin sauraron kararrrakin da aka daukaka daga manyan kotunan jihohi da na kasa da kuma kotunan sauraron kararrakin zabe.

’Yan Najeriya na zargin cin karo da juna a wasu hukunce-hukunce da Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta yanke kan wasu shari’o’in zabe masu kama da juna da aka daukaka zuwa gare ta a baya-bayan nan.

Hakan ya kawo zargin kotun na yi wa Dokar Zabe fassara daban-daban wajen yanke hukunci a kan shari’a iri guda lamarin da yake ci gaba da daukar hankali.

Hazalika soke hukuncin kotunan sauraron kararrakin zaben 2023 a wasu jihohi hudu da Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta yi ya sake jawo ce-ce-ku-ce da zargin rashin adalcin kotun daukaka kara.

Zaben Gwamnan Kano

A ranar 20 ga watan Satumba Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Jihar Kano ta kwaje kujerar Gwamna Abba Kabir Yusuf nan Jami’iyyar NNPP ta ba wa Nasiru Yusuf Gawuna na APC.

Kotun ta kwace kujearar Abba ne bayan soke 165,663 daga cikin kuri’unsa da cewa haramtattu ne saboda rashin hatimi da sa-hannun jami’in Hukumar Zabe (INEC) a jikinsu.

Bayan ta zabge kuri’un ne Gawuna da ya zo na biyu ya yi masa fintinkau don haka ta ayyana dan takarar na APC a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris.

Sai dai kuma kotun ta ce ba ta da hurumin yanke hukunci kan halascin zaman Abba dan takarar NNPP da masu kara (APC) suke kalublanta — saboda batu ne na kafin zabe.

Amma da Abba ya daukaka kara zuwa Kotun Dakaka Kara ta Tarayya da ke Abuja sai ta ce ai kotun farkon na da hurumin sauraron batun halastaccin takarar Abba.

Ta kuma yanke hukunci cewa Abba ba halastaccen dan takarar NNPP ba ne, saboda babu sunansa a rajistar mambobin jam’iyyar da ta mika wa INEC gabanin zabe.

Don haka ita ma ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben na gwamnan Kano.

Amma da ta fitar da kundin rubutaccen, sai aka ga ya tabbatar da nasarar Abba, da wasu abubuwa sabanin hukuncin da ta yanke, lamarin da ya haddasa rudani.

Magatakardar kotun ya bayyana cewa kuskuren rubutu aka samu, kuma bai shafi ainihin hukuncin da aka yanke ba, za kuma a iya gyara kuskuren bisa bukatar bangarorin da abin ya shafa.

Wannan lamari dai ya haifar da fargaba da zanga-zanga har ma da rikicin siyasa a Kano, inda NNPP ke zargin juya ainihin hukuncin kotun aka yi ta bayan fage.

A kan haka ne aka bukaci Majalisar Alkalai ta Kasa (NJC) sake nazarin hukuncin kuma ta yi da bincike kan abin da ya haddasa tufka da warwara a kundin hukuncin.

A ranakun 28 an yi dauki-ba-dadi tsakanin ’yan sanda da masu zanga-zangar rashin jin dadi da hukuncin kotun daukaka karar a Kano.

Zaben Filato

Ranar 22 ga Satumba Kotun Kararrakin Zaben Gwamnan Filato ta tabbatar da nasarar Gwamna Caleb Mutfwang na PDP ta kori karar da Nentawe Goshwe na APC ya shigar na kalubalantar takararsa kan rashin shugabancin jami’iyya da kuma saba dokar zabe.

Amma da Goshwe ya garzaya zuwa Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke Abuja, sai ta soke hukuncin kotun farkon ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga Marsi

Kotun a kwace kujerar Mutfwanga ne bisa dogaro da sashe na 177 na kudin tsarin mulki, cewa PDP ba ta gabatar da shi a matsayin dan takararta bisa tsari ba, kuma ta saba umarnin kotu na gudanar da zaben shugabanni a kananan hukumomi 17 na jihar, inda ta yi a guda biyar kacal.

Ta kuma bayyana cewa batun halascin tsayawa takara ya shafi kafin zabe da kuma bayan zabe, don haka kotun farko ta yi kuskuren cewa Goshwe ba shi da hurumin kalubalantar tsayawar Mutfwang takara.

Shi ma wannan hukunci ya kawo rudani da zargin rashin adalci, inda magoya bayan Mutfwang da PDP suka gudanar da zanga-zanga a garin Jos.

Sun bayyana kwarin gwiwa cewa za su samu adalci a karar da suka daukaka zuwa Kotun Koli; wasu kungiyoyin fararen hula ma su wa yi watsi da hukuncin da cewa kotun ba ta da hurumin sauraron batun kafin zabe.

A kan batun rashin zaben shugabannin jami’iyya ne kuma kotun daukaka karar ta kwace kujerun ’yan PDP hudu da ke majalisar dokoki ta kasa wasu 11 da ke majalisar jihar

Su ma ’yan majalisar da aka soke zaben nasu sun daukaka kara zuwa Kotun Koli kuma sun yi zargin wasu kusoshin APC na da hannu a hukuncin da kotun dakaka karar ta yanke.

‘Inconclusive’ a Zamfara

A shari’ar zaben Gwamnan Zamfara kuwa, Kotun Daukaka Kara ta Tarayya bayyana zaben ta yi a matsayin wanda bai kammala ba, ta kuma umarci INEC ta sake zabe a kananan hukumomi uku —Birnin-Magaji da Bukkuyum da kuma Maradun.

Kotun ta bayyana cewa kuskurene INEC ta dagaora da bayanan da ke shafinta na IReV ta tattara sakamakon zaben gwamnan jihar, don haka ta soke nasarar Gwamna Dauda Lawal Dare na Jami’iyyar PDP.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan tsohon gwamnan jihar, Bello Mohammed Matawalle na APC ya daukaka kara.

Hukuncin dai ya jawo ce-ce-ku-ce da zargi daga PDP da magoya bayan Dawal Lawal cewa kotun na nuna rashin adalci da kuma neman tauye tsarin dimokuradiyya.

Zaben Gwamnan Nasarawa

Ranar 5 ga watan Oktoba kotun zaben gwamnan Nasarawa ta kwace kujerar Gwamna Abdullahi Sule na APC ta ba wa David Ombugadu na PDP a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben.

Kotun ta bayyana cewa ba a tsayar da Abdullahi Sule takara ta halastacciyar hanya ba, domin ba ya cikin wadanda suka shiga zaben dan takarar gwamnan jihar da uwar jam’iyyar APC ta gudanar .

Don haka ta ba wa Ombugadu kujerarar a matsayin wanda ya zo na biyu a zaben mai cike da rudani.

Amma da Abdullahi Sule ya daukaka kara sai Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta soke hukuncin kotun farko ta tabbatar da nasararsa a ranar 23 ga watan Nuwamba.

Ta kuma bayyana cewa kotun farkon ta yi kuskure wajen dogaro da bayanan shaidu wajen soke zaben gwamnan domin batun daukar nauyi da tsayar da dan takara abu ne na kafin zabe wanda kotun sauraron kararrakin zabe ba ta da hurumin sauraron sa.

Haka shi ma wannan hukunci ya tayar da kura, Ombugadu da PDP da magoya bayansa suka yi watsi da hukuncin tare da zargin rashin adalci.