✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ZABEN BAYELSA: Harbin bindiga ya tarwatsa masu zabe a Opolo

Harbin bindiga ya tarwatsa masu kada kuri’a  a rumfar zabe ta unit 8 mazaba ta ward 5 da ke Opolo Karamar Hukumar Yanagoa jihar Bayelsa.…

Harbin bindiga ya tarwatsa masu kada kuri’a  a rumfar zabe ta unit 8 mazaba ta ward 5 da ke Opolo Karamar Hukumar Yanagoa jihar Bayelsa.

Wani ganau ya ce, bayan an tantance shi yana shirin kada kuri’arsa sai wasu ‘yan bindiga suka zo rumfar zaben suka tarwatsa jami’an zaben sannan suka kwashe takardun zaben.

Ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun kori masu kada kuri’ar sannan suka lalata wasu motoci da suke kusa da rumfunan zaben.

Wasu masu kada kuri’a sun ce, an kammala tantance su kenan zasu kada kuri’arsu, sai ‘yan bindigar suka fara harbi a rumfar zaben.