✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kano: Dahiru Bauchi ya nesanta kansa da wasikar ‘Neman Adalci’

Sheikh Dahiru Bauchi ya nesanta kansa da wasikar da ake riya cewa ya aike wa Babban Alkalin Najeriya kan Shari'ar Zaben Gwamnan Kano.

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman, ya nesanta kansa da wasikar da ake riya cewa ya aike wa Babban Alkalin Najeriya (CJN) kan Shari’ar Zaben Gwamnan Kano.

Sheikh Dahiru Bauchi ya karyata labarin da ke yawo a kafofin sada zumunta cewa shi ne ya rubuta wa babban alkalin wata wasika mai taken “Neman A Yi Adalci Nan Take” a kan shari’ar zaben gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna.

Mashahurin malamin ya ce ba shi ya rubuta wasikar ba, ba daga gare shi ta fito ba, sannan ba shi da masaniya a game da ita.

Da yake karin bayani a kan lamarin, Mataimakin Shugaban Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sayyadi Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi ya ce “An ja hankalinmu kan wasikar da aka ce an aike wa Babban Alkalin Najeriya.

“Jama’a daga sassa daban-daban na kira da nufin tantancewa su kuma tabbatar da gaskiya game da batun wasikar.

“Gaskiyar magana wasikar ba ta fito ne daga wajen Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba, takardar da aka rubuta wasikar a kanta ba irinta Sheikh Dahiru Bauchi yake rubuta wasika a kai ba.

“Marubutan sun yi jabun takardar da Mu’assasar Sheikh Dahiru suke rubutu a kai ne, kuma suka sauya mata fasali, sannan Sheikh din ba shi ne wanda yake sanya hannu a kan takardun da mu’assa ke rubutawa ba.

“Kuma a yau Sheikh ba ya sanya hannu a kan wata takarda in ya ce a rubuta, amma yana yin amfani ne da tambari na musamman a kan duk wata takarda da ta fito daga gare shi.”

Sayyadi Tijjani ya bukaci jama’a da hukumomin da abin ya shafa da su yi watsi da wasikar, su kuma fahimci cewa wasikar ba ta malamin ba ce, domin hasali ma, shi ba ya sa baki a duk wani abu da ke gaban kotu.