✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben Ondo: Jami’an tsaro sun yi awon gaba da ‘yan bangar siyasa 2

Jami’an tsaron sun ki su ce uffan a kan laifin da ake zargin matasan da aikatawa, ko da yake ana kyautata zaton ‘yan bangar siyasa…

Jami’an tsaro sun yi awon gaba da wasu matasa biyu da aka zarga da dakon wasu jakunkuna a bayansu a cibiyar tattara sakamakon zabe dake makarantar firamare ta Scared Heart a karamar hukumar Akure ta Kudu a jihar Ondo.

Mazabar dai ita ce wadda dan takarar PDP, Eyitayo Jegede ya kada kuri’arsa dazu da safe kuma tana da rumfuna har guda uku.

To sai dai jami’an tsaron sun ki su ce uffan a kan laifin da ake zargin matasan da aikatawa, ko da yake ana kyautata zaton ‘yan bangar siyasa ne.

An yi awon gaba da matasan ne a wata mota kirar bas mai lambar jihar Ekiti ta TUN 528 XA.

Yanzu haka dai ana zaman dar-dar a cibiyar musamman yadda ake hangen jami’an tsaro na ta karakaina dauke da makamai a yankin.

Tuni dai aka kammala kada kuri’a a yankin yayin da malaman zabe ke ci gaba da tantancewa da kuma kirga kuri’un.