✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaizayar kasa na hadiye gidaje a Kaduna

Mazauna Unguwar Zage-Zagi a Gundumar Rigasa da ke Karamar Hukumar Igabi sun ce suna cikin tashin hankali samakon yadda zaizayar kasa ke hadiye musu gidaje.…

Mazauna Unguwar Zage-Zagi a Gundumar Rigasa da ke Karamar Hukumar Igabi sun ce suna cikin tashin hankali samakon yadda zaizayar kasa ke hadiye musu gidaje.

Gidaje masu yawa ne suka ruguje sannan filayen suka zaizaye suka koma kamar ba a tava yin gini a kai ba.

Malam Musa Sarki wanda wakilinmu ya tarar da shi a kusa dai indagidansa yake ashekara biyu da suka wuce amma yanzu ya zama rami, ya ce ya zo ne domin duba yadda dakin da ya rage a gidan ya fadi sakamakon ruwan sama da aka yi a makonnin baya.

Yadda na rasa gidana’

Shi dai Malam Musa tare da matarsa da ’ya’ya bakwai sun tashi daga gidan ne a lokacin da ya lura cewa akwai hadari su ci gaba da zama a gidan, “Na bar gidan ne

shekara biyu da suka wuce kuma yau na zo ne don duba dakin karshe da ya rage a gidan bayan an sanar da ni cewa ya rushe sakamakon ruwan sama da aka yi cikin dare.

Yanzu babu gidan babu kuma filin duk sun zama rami,” inji shi.

A cewarsa, tun bayan barinsa gidan ya koma gidan wani abokinsa ne wanda ya ba shi xaki kafin Allah Ya hore masa kuxin haya tunda ba ya da halin gina wani gidan a yanzu.

“Yanzu qoqarin ciyar da iyalina nake yi sannan ina qoqarin samun wani gidan da zan kama haya, saboda gaskiya rayuwa a cikin wannan hali sai haquri,” inji shi.

Ba gidan Malam Musa ne kadai zaizayer qasar ta shafa ba, kamar yadda ya nuna ramin tare da cewa, “Duk wajen nan da kake ganin ya zama rami gidajen mutane ne a shekarun baya.”

Binciken da Aminiya ta yi, ta fahimci cewa zaizayar qasar ta fara ne shekara kusan bakwai da suka wuce amma abin ya fi muni ne a cikin shekara uku da suka wuce wanda har ta kai ga gidaje da yawa sun rushe.

Hakan ya tilasta wa mazauna unguwar suka riqa barin gidajensu domin ceto rayukansu da na iyalansu. Waxanda kuma suka ci gaba da zama, suna zama ne cikin dar-dar a kullum.

“Kamar yadda kake iya gani zaizayar na ci gaba da fadada domin kwanan nan gidan maqwabcina ya rushe amma muna godiya ga Allah shi da iyalinsa sun bar gidan. Kuma

har yanzu babu wani taimako da muka samu daga gwamnati duk da cewa waxansu ma’aikata sun zo domin duba yadda wajen yake, amma tunda suka tafi ba mu sake ji daga gare su ba,” inji Malam Musa.

Wakilinmu wanda ya zagaya unguwar ya lura cewa akasarin masu gidaje a yankin duk sun tashi sun bar gidajen musamman wadanda ke dab da ramin.

Wuraren da zaizayar ke ci gaba da yi musu varna sun haxa da Layin Couch kusa da makabarta daga Titin Daura sai Titin Kutungare da Titin Garba Waziri sai Titin Yahaya Dangaladima.

Zaizayar qasar ta kuma kai wasu layuka da ke yankin Shanono duk a Gundumar Rigasa.

A yanzu haka gidajen da zaizayar kasar ta shafe suna da yawa sannan akwai gidajen da suka tsage wasu kuma katangarsu duk ta fadi.

Sare itatuwa biyu ne ya jawo zaizayar’

Abdullahi Dan Sarki wanda ya taba zama a unguwar ya ce abin da ya janyo zaizayar kasar a yankin na Zage-Zagi shi ne sare wasu itatuwan mangoro biyu da aka yi.

“Na tuna lokacin da aka tumbuke itatuwan mangoron biyu da maqwabtanmu suka yi a yunkurinsu na jara fadin gidajensu.

Kuma a lokacin zan iya tuna wani tsoho da ya nuna kada a sare itatuwan ammamutanen suka ki ji.

“Tun daga sare itatuwan ne abinda ya fara ra ci kadan-kadan har ta kai ga yin wannan barna. Kuma ina tabbatar maka cewa duk wanda ya zauna a unguwar shekara 10 da suka wuce zai tabbatar da labarin da na fada.

“A lokacin haya nake a daya daga cikin gidajen da ke wajen amma yanzu gidan da na zauna ya rushe koda yake na tashi daga gidan tun kafin ya gama rushewa,” inji shi.

Masana harkar muhalli sun ce sare itatuwa ba bisa ka’ida ba na janyo zaizayar qasa.

Hankalinmu a tashe yake’

A yanzu haka akasarin jama’ar da ke zaune a yankin sun ce suna cikin damuwa tare da rashin kwanciyar hankali sakamakon

yadda zaizayar kasar ke ci gaba da lalata gidajen da suka saura.

Wani dattijo mai suna Ibrahim Isiyaku ya ce hankalinsu ba a kwance yake ba, musamman duk lokacin da aka yi ruwan sama.

“Gidajenmu na cikin hadari saboda wannan zaizayar da ke damunmu. Dubi yadda ramin ke ci gaba da fadada. Gaskiya muna neman taimako,” inji shi.

Shi kuwa Malam Abdullahi Muhammad cewa ya yi ba su da inda za su koma kuma babu mai son sayen gidajen da ke unguwar domin babu mai san yin hasara.

Idris Sadiq wani mazaunin yankin ya ce ramin da ke wajen na zama rafi musamman a lokacin damina. “Idan ka zo wajen nan idan

aka yi ruwan sama sai ya ba ka tsoro saboda yadda yake komawa rafi,” inji shi.

Sakataren Kungiyar Ci Gaban Zage-Zagi, Abdulrahman Abdulkareem ya nuna wa

wakilinmu wasikun da suka rubuta wa duk ma’aikatun da abin ya shafa domin sanar da su halin da ake ciki a yankin. Ya ce sai dai har yanzu ba su samu wani taimako ba daga gwamnati da hukumomin wanda hakan ke damunsu musamman ganin yadda zaizayar kasar ke ci gaba da rusa gidaje.

Daga cikin ma’aikatun da suka aike wa wasiku akwai Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kaduna da Hukumar Kula da Zaizayar Kasa da Ma’akatar Gidaje da Ci Gaban Jihar Kaduna wadanda har sun ziyarci wajen domin gane wa idonsu.

Ya kara da cewa sun aika wa ofishin xan majalisa mai wakiltarsu a Majalisar Wakilai da ofishin Ministan Muhalli da ke Abuja sun sanar da su halin da ake ciki.

Muna kokari kan lamarin – Ma’aikatar Muhalli

Aminiya ta samu zantawa da Daraktan Kula da Muhalli a Ma’aikatar Kula da Muhalli ta Jihar Kaduna, Alhaji Mu’azu Usman wanda ya ce ma’aikatar na sane da abin da ke faruwa a yankin na Rigasa.

A cewarsa akalla akwai wurare da ke fama da zaizayar qasa 143 a kananan hukumomi 23 da ke jihar kuma ma’aikatar na kokarin ganin ta magance matsalar duk da cewa magance irin wannan matsala na da tsadar gaske.

“Jihar nan kadai ba za ta iya magance matsalar ba, don haka dole sai mun nemi taimakon sauran ma’aikatu da hukumomi.

Amma a yanzu muna ci gaba da tattara bayanan irin waxannan wurare kuma cikin wuraren da muka tatttara bayanansu har da na yankin Kutungare a Rigasa,” inji shi.

Ya ce hakikanin gaskiya ma’aikatar na kokarin ganin yadda za a magance matsalolin zaizayar kasa a fadin jihar.

Don haka ya shawarci jama’a su kauce wa yi wa kasa ta’adi ta hanyar sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ka iya janyo zaizayar kasa.