✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan dinke barakar da ke tsakanin Gwamnati da Kiristocin Kaduna — Uba Sani

Na lura cewa akwai tsamin dangantaka tsakanin al’ummar Kudancin Kaduna da gwamnatocin da suka shude.

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta daura damarar dinke duk wata baraka da ke tsakanin gwamnati da al’ummar Kudancin Kaduna.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a sakonsa ga kungiyar shugabannin Kiritoci da malaman majami’u, a yayin wani taro da suka gudanar a Majami’ar Throne room da ke garin Kafanchan.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban mataimakinsa na musamman kan harkokin addinin Kiristoci kuma malamin majami’ar Baptist da ke Kaduna, Rabaran Dokta Ishaya Adamu Jangado, ya ce ya tarar da tsamin dangantaka tsakanin al’ummar Kudancin Kaduna da gwamnatocin baya, saboda haka yake son ganin ya dinke barakar.

Uba Sani ya kuma bukaci hadin kan jagororin mabiya addinin Kirista, domin ciyar da Jihar Kaduna gaba.

Tun da farko, shugaban taron, Afostil Dokta Emmanuel Nuhu Kure, ya gode wa gwamnan da ya ke kokarin neman hadin kansu, inda ya ce sun dau alkawarin bashi gudunmawa domin ciyar da jihar su gaba.