✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan kawo karshen ’yan bindiga cikin kankanin lokaci —Tinubu

Tinubu ya kai ziyara Birnin Gwari duk da kaurin sunan yankin wajen hare-haren ’yan bindiga...

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya shirya tsaf don kawo karshen ’yan bindiga, matukar aka zabe shi a matsayin angon Najeriya a 2023.

Tinubu, ya bayar da wannan tabbaci ne yayin ziyarar da ya kai Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna, don jajanta wa al’ummar yankin kan hare-haren ’yan bindiga.

“Na tsaya a gabanku ne don tabbatar muku cewa wata damar na tafe; Zabe ya matso.

“Mun shirya yakar ’yan bindiga kuma ba za mu gajiya ba har sai mun ga bayansu; ina ba ku wannan tabbaci,” in ji shi.

Tinubu ya jajanta wa Sarkin Birnin Gwari, Mallam Zubairu Maigwari, kan irin matsin rayuwa da ’yan bindiga suka jefa yankin.

Ya ce ziyarar na daga cikin wani shiri na musamman da suka ware don duba halin da yankin ke ciki da kuma nemo bakin zaren yadda za a inganta a rayuwar mutanen yankin.

A nasa bangaren, Sarkin ya jinjina wa dan takarar na APC na namijin kokarin da ya yi na kai ziyara yankin duk da irin matsalar tsaro da ake ciki.

Tinubu ya ziyarci Birnin Gwari ne a mota duk da irin matsalar rashin tsaro da yankin ke fama da ita.

Daga cikin ’yan rakiyarsa, har da abokin takararsa, Kashim Shettima da gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, da Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da sauran ’yan kwamitin yakin zaben APC.

Karamar Hukumar Birnin Gwari na daga cikin yankunan da suka fi fuskantar munanan hare-haren ’yan bindiga a Jihar Kaduna.