✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zanga ta barke kan tsadar kayan abinci a Neja

Jama'a na ci gaba da nuna bacin ransu kan yadda kayan abinci ke tashin gwauron zabi.

Dandazon mutane sun mamaye Minna, Babban Birnin Jihar Neja, don nuna bacin ransu kan yadda kayan abinci ke ci gaba da tashin gwauron zabo.

Tun misalin karfe 7 na safiyar ranar Litinin, dandazon mutane suka yi tsinke suka tare hanyar Minna zuwa Bida, don nuna bacin ransu kan tsadar kayan abinci.

Hakan ya kawo tsaikon zirga-zirgar ababen hawa a birnin.

Jami’an ’yan sanda kawo dauki domin tabbatar da tsaro, amma wasu masu zanga-zangar suka yi kokarin kawo musu farmaki, lamarin da ya kai ga tarwatsa su da harbin bindiga.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Ibrahim Gana, ya koka kan yadda ake sayar da kwanon shinkafa Naira 2,000 a kasuwanni, yayin da masara ta kai Naira 1,000.

“Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin rage wahalhalun da talakawan Najeriya ke sha, mutane ba za su iya jurewa ba.”

Kakakin rundunar, DSP Wasiu Abiodun, bai amsa kiran waya don yin karin haske kan lamarin ba.

Kayan masarufi na ci gaba da yin tashin gwauron zabo a Najeriya, lamarin da ya sanya talakawa yin kira ga shugabanni su kawo musu dauki.

A makon da ya gabata a Jihar Kano, masu sana’ar gurasa sun yi zanga-zanga tare da shiga yajin aiki kan tsadar fulawa.

Masu sana’ar sun koka kan cewar tsadar kayan sarrafa gurasa na barazana ga rayuwarsu a jihar.