✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin Damfara: Kotu ta hana a tura Abba Kyari zuwa Amurka

Kotu ta ce haram ne tura wanda ake zargi domin fuskantar shari'a a wata kasa muddin yana fuskantar shari'a a kasar da yake zaune

Babbar Kotun Tarayya ta yi watsi da bukatar tura fitaccen dan sanda da aka dakatar, DCP Abba Kyar, zuwa kasar Amurka domin fuskantar Shari’a kan zargin damfara ta intanet.

Alkalin kotun da ke zamanta a Abuja, Mai Shari’a Iyang Ekwo ya yi watsi da bukatar ce a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa babu yadda za tura Abba Kari wata kasa domin fuskantar Shari’a, alhali yana fuskantar shari’a a Najeriya, wanda Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) suka yi karar sa.

Ya ce dokar tura wanda ake zargi domin fuskantar shari’a a wata kasa ya haramta tura wanda ake zargin muddin yana fuskantar shari’a a kasar da yake zaune.

Don haka kotun ta yi watsi da bukatar.

Karin bayani na tafe.