✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin N37bn: Sadiya ta kai kanta EFCC

Tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouq, ta kai kanta ofishin Hukumar EFCC domin amsa tambayoyi kan zargin badakalar Naira biliyan 37

Tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouq, ta isa ofishin Hukumar yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) domin amsa tambayoyi kan balakalar Naira biliyan 37.

Ana tuhumar tsohuwar ministan a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ce kan badakalar Naira biliyan 37 da ake zargin wani dan kwangila mai suna James Okwete ya karkata.

A safiyar Litinin Sadiya ta rubuta a shafinta na X cewa, “Ni da kaina na isa hedikwatar EFCC domin amsa gayyatarta ta neman karin haske kan wasu batutuwan hukumar tana bincike.”

Sadiya ta kai kanta oifshin hukumar ne bayan a makon jiya ba ta samu zuwa ofishin domin amasa tambayoyin hukumar game da zargin badakalar ba.

A makon jiya Sadiya ta bayar da uzurin rashin lafiya a matsayin dalilin rashin amsa gayyatar da EFCC ta yi mata.

Bayanai sun ce tsohuwar ministar, ta nemi EFCC ƙara mata lokaci kan gayyatar titsiye da za a yi mata bisa zargin ta da hannu a badaƙalar Naira biliyan 37 tare da wani dan kwangila, James Okwete.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya ce, tsohuwar ministar ta aiko lauyanta a matsayin wakili tare da neman karin lokaci domin amsa gayyatar, tana mai ba da uzuri na rashin lafiya.

A makon jiya ne, Sadiya Umar Farouq ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ta musanta hannu a badaƙalar da ake zargi.

Ta kuma yi iƙirarin cewa kwata-kwata ma ba ta san ɗan kwangilar da rahotanni ke cewa hukumar EFCC ta kama a binciken da take yi dangane da batun ba.