✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zariya: Yadda ’yan bindiga suka sace mutum 6 a Wusasa – Basarake

Ya ce wannan shi ne kusan karo na biyar da ake kai wa yankin nasa hari.

Sarkin Wusasa da ke Zariya a Jihar Kaduna, Injiniya Isiyaku Danlami Yusufu, ya ce kusan sau biyar kenan ’yan bindiga suna kai wa yankinsa hari, suna kashe mutane sannan su yi garkuwa da wasu.

Basaraken ya bayyana haka ne lokacin da yake zanta wa wakilin Aminiya a kan yadda maharan suk yi awon gaba da mutum shida a yankin ranar Asabar.

Aminiya ta rawaito cewa a daren ranar Asabar ne wasu ’yan bindiga da ba a san adadinsu ba suka kai hari unguwar Kuregu da ke yankin na Wusasa, inda sukayi awon gaba da mutanen, cikinsu har da iyalan wani dan sanda kwantar da tarzoma.

Masu garkuwa da mutanen sun far wa unguwar ne a yayin da ake gudanarwa da bikin Kirsimeti.

A cewar basaraken, “Wannan shi ne karo na biyar da ’yan bindigar ke far mana.

“Su kan shiga yankin su kashe mutane su yi garkuwa da wasu, sai dai a wannan karon babu wanda ya rasa ransa, sun dai kwashi mutane takwas, bayyan sun yi tafiya mai nisa, sai suka sako yara biyu.

“Cikin wadanda suka tafi da su akwai matar wani Sufeton dan sanda mai suna Ibrahim Diboga sun tafi da matarsa mai suna Alheri, da ’yarsa mai suna Afan, sai matar wani dan sandan kwantar da tarzoma wanda yake aiki a Legas mai suna Kyauta.

“Daga bisani sun sako ’yarta mai shekara hudu kamar yadda na fadama, sai magidanci mai suna Joseph, Samuel da matarsa, da sauran,” inji Injiniya Isyaku.

Sarkin na Wusasa ya ce tuni suka sanar da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, wanda kuma ya ce musu sun dukufa wajen ganin sun ceto su.