✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Zazzabin Lassa ta kashe likitoci 2 a Nasarawa

Likitoci biyu da matar aure da karamin yaro ne cutar ta kashe, kasa da mako guda da bullarta a jihar

An shiga cikin zullumi bayan cutar Zazzabin Lassa ta kashe mutu hudu, ciki har da likitoci biyu da wata mata da karamin yaro a Jihar Nasarwa.

A makon jiya ne Aminiya ta kawo rahoton da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nasarawa ta sanar da sake samun bullar cutar mai kisa a jihar.

A ranar Juma’a ce Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Dokta Janet Angbazo, ta ce “An tabbatar da kamuwar mutum biyu, akwai wasu uku kuma da ake zargi sun harbu da cutar kuma ana lura da su a cikin jihar nan.”

A cewarta wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar an kwantar da su ne a wani asibiti a Abuja, sannan ta gargadi jama’ar jihar ta su yi hattara da kamuwa cutar.

Da take sanar da haka ranar Juma’a, ta bayyana cewa an dauki samfurin jinin karin wasu mutane da ake zargi da kwayar cutar zuwa dakin gwaje-gwajen Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) domin tantancewa.

Gwamnatin jihar, a cewarta, tana shirin fara yi wa mutane gwajin kwayar cutar Zazzabin Lassa a cibiyar binciken cututtuka masu yaduwa ta jihar (NASIDARC).

— Alamomin cutar Zazzabin Lassa

“Alamomin cutar sun hada da zazzabi na mako daya zuwa mako uku bayan kamuwa da kwayar cutar.

“Kashi 80 cikin 100 na alamomin cutar Lassa ba su bayyana ta yadda za a iya gane su.

“Kashi 20 cikin 100 na masu cutar na iya fama da zazzabi mai tsanani, sarkewar numfashi, amai, jijjiga, kumburin fuska, da kuma ciwon kirji da baya da mara.

“Cutar na iya yin kisa a sakamakon daina aikin wasu sassa na jikin dan Adam,” kamar yadda ta bayyana.

Don haka ta shawarci jama’ar jihar da su dauki kwararan matakan kariya ta hanyar nisantar masu cutar gami da tabbatar da tsaftar muhalli domin kawar da beraye da dangoginsu.