✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Zulum ya bai wa asibiti tallafin N100m da gidaje 24

Zulum ya bai wa Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiduguri (UMTH) tallafin Naira miliyan 100.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya bai wa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) tallafin Naira miliyan 100.

Zulum ya kuma aza harsashin gina gidajen ma’aikata 24 masu farko da dakuna uku-uku da za a kammala a cikin wata shida a asibitin, wanda mallakin Gwamnatin Tarayya ne.

Da yake mika cekin kudin tare da kaddamar da aikin gina gidajen ma’aikatan lafiyar a ranar Juma’a, Zulum ya ce Gwamnatin Jihar Borno na yin haka ne a matsayin gudunmawarta, saboda kokarin asibitin wajen dawainiyar jinyar dubban mutanen jihar.

Ya ce shi ya sa zai fitar da kudade da wuri ga dan kwangilar aikin ginin domin rage matsalar gidajen likitoci a asibitin da kuma kawo su kusa da marasa lafiya.

Da yake jawabi a yayin karbar cekin kudin, Shugaban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, Farfesa Ahmed Ahidjo, ya yaba wa Gwamna Zulum, bisa taimakon da yake wa asibitin wajen samar da kayan aiki.

A cewarsa, irin gudunmawar da gwamnatin ta saba bai wa asibitin, abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba.