✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zulum ya bankado ma’aikatan bogi 22,556 a Borno

An samu rarar Naira miliyan 420 bayan kawar da ma'aikatan bogin

An bankado malamai da ma’aikatan bogi guda 22,556 a Jihar Borno bayan binciken da Gwamna Zulum ya ba da umarni.

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton da kwamitin binciken karkshin Sanata Kaka Malam Yale da kuma kwamitin malaman firamare karkashin jagorancin Dakta Shettima Kullima suka gabatar wa gwamnan Zulum.

Daga ciki an samu mutum 14,762 a kan tsarin biyan albashi na ma’aikata, sai mutum 7,794 da aka gano malaman bogi ne.

Bayan gano manakisar, an samu rarar Naira miliyan 420 da suka had da miliyan N183.6 daga malaman bogi, sai kuma miliyan N237 daga sauran ma’aikatan bogin.

Dakta Kullima ya ce kafin binciken jihar na malaman firamare 26,450 a kananan hukumomi 27, amma guda 24,250 ne daga cikinsu kwamitin ya tabbatar.

Ya kara da cewa ragowar mutum 2,204 sun ki bayyana gaban kwamitin domin tantance sahihancinsu.

Shi kuwa Sanata Yale cewa ya yi, bayan gudanar da bincike adadin ma’aikatan ya sauka daga 71,568 zuwa 56,806.

Bayan karbar rahoton, Gwamna Zulum ya ce binciken na da kyau domin kyautata tsarin al’amuran kananan hukumomi a jihar.

Ya kara da cewa shi ma bangaren ilimi an yi hakan ne don tabbatar da gyara a cikinsa.

Daga karshe ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa marayu da marasa karfi, don daukar nauyin karatunsu.