✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya rage wa manoma farashin man fetur

Gwamnan ya yi alkawarin raba injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana da irin shuka da takin zamani

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce zai rage wa manoma a yankin Damasak kudin fetur domin bunkasa samar da abinci a jihar.

Zulum, da ya yi alkawarin  raba wa manoma injinan ban ruwa masu  amfani da hasken rana da irin shuka da takin zamani da sauransu domin ganin Jihar Borno ta zama mai dogaro da kanta wajen samar da abinci.

“Domin ganin dorewar hakan, muna daukar matakan bunkasa noma tare da rage matsalolin tattalin arziki da manoman yankin Damasak suke fuskanta.

“Babban makamashin na’urorinsu na noma shi ne man fetur, saboda hakan nan ba da jimawa ba zan ba su tallafin domin magance wannan kalubalen.

“Gwamnati za ta tantance gidajen mai guda biyu da manomanmu za su rika zuwa su sayi fetur a kan farashi mai rahusa domin a samu saukin noma.

“Sannan za mu raba injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana da irin shuka da takin zamani da ma sauran kayayyakin amfanin gona ga manoma.

“Kuma Gwamnatin Jihar Borno za ta samar da injinan yayyafa ruwa masu amfani da hasken rana a wannan garin,” in ji Zulum.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Damasak, daya daga cikin yankunan manoma da ’yan ta’addar Boko Haram suka fi fama barna a jihar, amma yake arfadowa bayan rikicin na shekaru 13.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a garin, inda ya kwashe kwanaki biyu yana kula da rabon kayan abinci ga zawarawa da mata masu karamin karfi.