✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘2023: Arewa za mu sake ba takarar Shugaban Kasa a PDP’

Ba jam’iyyarmu ce ke mulki yanzu ba, mu ’yan adawa ne. Me ya sa mutane suka damu da abin da jam’iyyar adawa ke yi ba…

Tsawon shekaru 18, Alhaji Adamu Maina Waziri ya kasance mamba a Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP. A cikin wannan tattaunawar, tsohon Ministan Harkokin ’Yan Sanda zamanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ce yankin Arewa za su mika tikitin takarar Shugaban Kasa a 2023 saboda akwai yarjejeniyar da suka cimma a kan haka.

An fara shiga-da-fita kan zaben 2023, inda wadansu jiga-jigan PDP ke matsawa kan a ba Arewa takarar Shugaban Kasa, wadansu na adawa. Wace shiyya kake jin za ta fitar da dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyarku?

Ba jam’iyyarmu ce ke mulki yanzu ba, mu ’yan adawa ne. Me ya sa mutane suka damu da abin da jam’iyyar adawa ke yi ba jam’iyyar da ke mulki ba? A yau abin da ya dame mu kai-tsaye, kashi 51 cikin 100 shi ne na katabus ko rashin katabus na jam’iyya mai mulki.

Kila kuma kashi 49 na lokacin kan katabus ko rashin katabus na jam’iyyar adawa. Saboda haka kamata ya yi mu damu da abin da jam’iyya mai mulki ke yi. Tunda aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999, yau shekara 22, PDP ta yi shugabannin kasa uku a shekara 16; Shugaba Obasanjo, wanda baki ya zo daya kan a sanya shi a siyasa, kuma aka jefa masa kuri’a aka zabe shi, saboda a wancan lokaci ana bukatar irin Obasanjo a Najeriya, domin muna neman wani wanda zai gyara kasar, ya maido ta kan yadda take ciki a baya na kyakkyawan shugabanci da haxin kai.

Kuma ya yi bakin kokarinsa, sai dai a Najeriya wajibi ne mutane su tuna cewa dalilin da ya dawo da shi kan mulki shi ne kasancewarsa Kirista kuma dan Kudu. Bayan ya kammala wa’adinsa wajiba ne magajinsa ya zamo Musulmi dan Arewa. Hakan ya kawo (Umaru) ’Yar’aduwa wanda ya fara rashin lafiya a daidai lokacin da ya karbi shugabancin kuma ya zo ya rasu.

Don ci gaba da tafiyar da tsarin sai Mataimakinsa ya karbi ragama, dab da karewar wa’adin mulkinsu. Zabin da ke ga Najeriya a lokacin shi ne, akwai bukatar mutane su tuna cewa shi Mataimakin Shugaban Kasa ne mai kokari da biyayya da hakuri.

A shekarar 2011 za mu iya hana shi takara mu kawo wani ya amshi ragama ko mu kyale shi ya ci gaba. Ina jin kyakkaywan tunani shi ne a bar shi ya ci gaba, kuma ina daga cikin wadanda suka goyin bayan sake zabarsa a shekarar 2011 bisa lura da hakan.

Kuma bisa wata rubutacciyar yarjejeniya ko fahimtar juna, Shugaba Jonathan zai yi zango daya ne ya gyara wasu ’yan kurakurai da suka zama sanannu a mulkin Najeriya.

Wadanne kurakurai ne?

Su ne wa’adin Shugaban Kasa da Gwamna shekara hudu ne sau biyu. Za ka iya samu Shugaban Kasa ko Gwamna bai aikata komai ba a zangon farko domin yana karbar mulki ne a tsakiyar shekara, kuma bayan wata shida sai a shiga sabuwar shekara. Sannan bayan shekara biyu zai fara tunanin yakin neman zabe na gaba.

Shugaba Jonathan ya dauki alkawari kuma ya bayyana wa jama’a cewa zai gyara tsarin mulki ta yadda wa’adin zai kasance sau daya. Shekara biyar ko shida ya fi dacewa kuma zai sake fasalin harkokin zabe. Wannan saboda yana ganin tsarin da ya kawo gwamnatoci a 2003 zuwa 2009 ya sha suka a wurin kotuna da masu sanya ido kan zabe.

Za a sake sauya dokar zabe kuma zai gudanar da ayyuka da dama. Amma saboda wasu dalilai sai Shugaba Jonathan ya ki yin haka, wanda hakan ne ya jawo faduwar Jam’iyyar PDP a 2015, duk da cewa akwai wasu dalilan da suka taimaka kuma tsarin ya rushe. A tsarin PDP, shugabanci zai gusa Arewa, saboda wanda zai gaji Shugaba Jonathan a 2011 wajibi ne ya zama dan Arewa ba Jonathan ba. Wannan shi ne yarjejeniyar PDP kuma shi ne na goyi baya.

Ba za mu tilasta wa APC wannan tsari ba haka su ma APC ba za su tilasta wa PDP nasu tsarin ba. Muna da wasu boyayyun abubuwa a PDP kamar yadda za su iya samu a APC. Ana sa rai a APC magajinsa (Buhari) ya zamo dan Kudu kuma Kirista.

Duk da cewa a nawa ra’ayin Obansanjo ya zo ne saboda wannan dalili, kasar tana bukatarsa, tana bukatar wani mutum mai gogewa irinsa. A shekarar 2011, yanayi ya sa an ce a bar shugaban da ke kai ya ci gaba. A shekarar 2015 kyawawan halayen da ake tsammani daga Shugaba Buhari suka sa ya kada Shugaba Jonathan.

Wajibi ne mutane su nemo shugaban mai inganci su yi watsi da wasu siffofi na yankin da ya fito ko addininsa da sauransu. Yanzu abin takaici mutanen Kudu maso Gabas suna gaya min cewa in ba a ba Ibo Shugaban Kasa ba, Najeriya za ta rushe.

To ku kawo min masu son tsayawa takara 10 ko fiye mu zaba daga ciki. Don haka idan za mu yi dimokuradiyya ce, mu yi ta don karfafa ginshiqan dimokuradiyyar, a tsare su mu zakulo shugaban mai da zai kasance alheri ga kasa.

Ba zan damu ba in yi takara da kowane mutum a matsayina na dan siyasa idan na bayyana sha’awata ta tsayawa takara, ya rage min in nemi kuri’un jama’a da za su sa in yi nasara. Idan ban nema ba, na fadi shi ke nan. Shugaba Obama ya yi haka kuma an sake zabensa.

Yallabai muna maganar Shugaban Najeriya ne ba Shugaban Qasa na PDP ba. Shin zai zama adalci Arewa ta sake rike kujerar Shugaban Kasa a 2023?

A Jam’iyyar PDP, adalci ne saboda za ka yi magana ce a mataki uku. Na farko magoya bayan jam’iyya, sai dan takarar Shugaban Qasa na PDP sannan magana a kan Shugaban Najeriya.

Yanzu idan ka yi magana da ni zan yi magana da kai ne kawai a matsayina na dan PDP saboda ba mu da alaka da shugabancin gwamnatin APC. Eh, zai iya zama Shugaban Kasa, amma ba dole ya zama na jam’iyya ba, amma dole ya zamo yana da jam’iyya.

Laimar ita ce jam’iyyarmu, saboda muna son mu ci zabe muna da tarihi cewa Shugaban Kasa na karshe shi ne Jonathan sannan Shugaban Kasar da zai zo ya zama dan takarar PDP, bari in sake cewa mu watsar da cewa PDP tana son tsayar da dan takarar da zai iya cin zaben Shugaban Kasa.

Idan lokacin ya zo wata bukatar na iya tasowa ta yi tasiri ga shawarar da za a yanke. Amma a kashin kaina zan goyi bayan a ce dan takarar ya fito ne daga Arewa.

Akwai rade-raxin cewa kuna kokarin dawo da tsohon Shugaban Kasa Jonathan a matsayin dan takarar jam’iyyarku?

A,a ba gaskiya ba ne, babban dan jam’iyya ne a PDP kuma mamba na Kwamitin Amintattu. Ban taba halartar wani taro ko aka gayyace ni ko kuma na ji wani sahihin labari kan cewa za a bai wa Jonathan tikiti a jam’iyyar ba, kuma ban yarda cewa Jonathan zai yi takara a Jam’iyyar PDP ko APC a 2023 ba, mutumin da kasancewarsadxan kasa mai cikakken hankali mai kamala da dattaku da a 2015 ya yarda da ya sha kaye a zabe.

Mutumin da ya sha caccaka daga jam’iyya mai mulki, kuma yake da wasu abubuwa masu kyau da marasa kyau da za a yi amfani da su wajen bata shi. Bai yi tsammanin zai kai wannan kujera mafi girma, kuma a ce yanzu ya dawo yana nema. Ban yi tsammani zai yi haka ba.

Ina jin an ba shi shawarwari mafiya dacewa cewa ya samu rabonsa kuma yana samun dimbin girmamawa bayan yin ritayarsa.

A Kudu, akwai jiga-jigan jam’iyyarku da suke ganin an ba Arewa takara a 2019, jam’iyyar ta sha kaye. Don haka a wajensu hakan ya kawar da batun karba-karba a jam’iyyar. Me ya sa ba za ku mara musu baya su samu a 2023 ba?

Na goyi bayan Atiku Abubakar ne a 2019 a zaben fitar da gwani, ba wanda ya ba shi tikiti, ya yi ta fadi-tashi ne ya samu nasarar tsayawa takara a PDP. Jam’iyyar PDP ba tana neman dan takarar Shugaban Kasa ba ne tana neman Shugaban Najeriya ne, wani ya samu takara a Jam’iyyar PDP amma ’yan Najeriya ba su zabe shi Shugaban Najeriya ba, wanda shi ne abin da take son cimmawa.

Don haka tikitin bai yi aikinsa ba ko kammalu ba. Kana so ka ce Atiku ya yi takarar ne a 2013? Me zai hana zai ina nema, akwai wadansu ma da dama da suke son su nema. Ni dan siyasa da ya amince a yi ta shiga zabe. Mutane su rika gabatar da kansu ga masu kada kuri’a su amince da sakamakon zaben. Idan ba su amince da sakamakon ba za su iya kalubalentarsa a kotu kamar yadda doka ta tanada a Najeriya.

Mutane su daina neman tikiti su nuna sha’awar neman kuri’un da za su sa su yi nasara. Wannan shi ne dimokuradiyyar. Ba na son jama’a su rika maganar son rai da wasu kananan abubuwa. A kowane lokaci mu zabi mutum mai nagarta ya zama Shugaban Najeriya. Ba za mu san mutum ba sai an bar fili a bude jama’a su zo su nuna kwarewarsu, a lokacin za mu gane inda suka nufa kuma mu auna dan takara bisa bukatun kasa.

Misali mutane suna zargin wannan gwamnati da nuna bambanci yanki, zai iya zama gaskiya ko akasin haka. Don haka a 2023 wa muke nema? Muna neman dan takarar da Najeriya ce a gabansa da ya san lungu da sakonta. Kuma wanda ya san jama’ar Najeriya a kowane lokaci kuma a kowace karamar hukuma da sa iya tsaya masa. Mutumin zai iya kiransa ya ba shi shawarar da za ta amfani kasa.

Kana ganin PDP za ta iya kada APC a 2023?

Ina son PDP ta karbi shugabancin kasar ba ma shugabanci kadai ba har da sauran jihohi a 2023, amma sai mun yi aiki don hakan. Ba tsuntsu ne daga sama gasasshe ba. Tilas ne mutane su yi aiki kan haka don su samu canji. Akwai abubuwa da dama na PDP da APC da za iya alkalanci da su ga jam’iyyun.

An zarge mu da miyagun abubuwa a shekara 16, wadannan mutane suka zo za su yi shekara takwas, sun samu gagarumar nassara ko akasi, za mu yi aunawa mu gani. Ba za mu ce don PDP ta yi shekara 16 APC ma ta yi shekara 16 ba. Idan PDP ta yi shekara 16 tana mummunan shugabanci ba, za mu bar APC ta yi mafi munin shugabanci ne? A’a ba za mu yi haka ba.

Mutane suna zargin cewa a 2019 ka sayar da yankinka da kake rike da shi tun 1999 ga Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe. Me za ka ce kan haka?

Ba haka ba ne. Mai Mala dan PDP ne daga 1999 zuwa 2004, inda ya taba kasancewa kansila, matashi ne da ke mutunta ni shi ne gaskiyar magana, batun gaskiya shi ne takarata a PDP a 1999 zuwa 2015 ne ya sa nake lashe zaben yankina. A 2019 an hana ni takara daga shugabannin jam’iyya inda aka ce ’yan Majalisar Wakilai suna da ’yancin kin amincewa, wannan ya saba wa dimokuradiyya.

Kuma bai yi mini da magoya bayana dadi ba. Lokacin da muke cin zaben ba mu samun tallafi amma muna hada kai mu cimma haka a mazabata. Lokacin da mutane suka yi amfani da guragun dalilai suka tilasta dan takara, sai mutane suka turje.

Na biyu ba jam’iyyarmu ce ke mulki ba. Sannan na bata wa mutane da dama hatta a sarakunan yankin da wadansu ma’aikatan gwamnati. Wadanda suka ci zaben sun san suna zaune ne a kan kusa. Kuma na yanke shawarar ba zan sake tsayawa takara ba, amma na shirya kwato hakkina a PDP a 2023.