✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Magoya bayan Tinubu na taron rantsar da shugabannin jihohi

Tinubu na da muradin neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Kungiyar magoya bayan Jagoran jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu, ya nemi takarar a kujerar shugaban kasa (TSG) na gudanar da taron kaddamar da shugabanninta na jihohi.

Taron da ke gudana a sakatariyar kungiyar ta kasa da ke Abuja ranar Asabar zai baje kolin ayyukan Tinubu tare da rantsar da shugabannin kungiyar na jihohin Najeriya 36.

Tinubu wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne yana da muradin  tsayawa takarar shugaban kasa domin maye gurbin Shugaba Buhari a zaben 2023.

Aminiya ta ga dandazon kungiyoyin magoya bayan Tinubu daga sassan Najeriya, daga kowane yanki, sun yi wa wurin taron tsinke.

Taron na zuwa ne mako biyu bayan dawowar jagoran na APC na kasa daga kasar Birtaniya inda ya shafe watanni yana jinya bayan an yi masa aiki.

Dan Majalisar Wakilai, Hon. James Abiodun Faleke, na daga cikin manyan masu jawabi a wurin taron.