✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya haramta bangar siyasa da dabanci

Gwamnatin Borno ta ce babu gudu, babu ja da baya a dokar.

Gwamnatin Jihar Borno ta haramta duk nau’ikan bangar siyasa da dabanci ko daukar makami ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta ce duk wanda aka kama yana bangar siyasa ko ya dauki kowane irin makami ba tare da izini ba zai yaba wa aya zaki.

“Duk matashin da ya kuskura aka kama shi da makami ko miyagun kwayoyi, sai ya yaba wa aya zaki. Allah Ya san manufarmu; ci gaban al’umma muke so mu kawo,” inji sanarwar gwamnatin jihar.

Kwamishinan Wasanni da Harkokin Matasa da Samar da Ayyukan Dogaro da Kai na jihar, Sa’inna Buba, ya ce Gwamnatin Zulum ba za ta lamunci duk wani rikici ba da matasa ke yi da sunan dabanci ko bangar siyasa.

A cewarsa, kafin fitar da sanarwar sai da Gwamna Babagana Zulum, tare da Kwamishinan ’Yan Sanda da Darakan hukumar DSS da Kwamandan hukumar Sibil Difens na jihar suka yi zama da shugabannin matasa.

Ya ce an yi zama da shugabannin matasan su 186 ne lura da karuwar rikice-rikicen matasa da ake samu a garin Maiduguri, inda dama can an riga an haramta dauka ko ajiyar makami.

Ya ce, “Saninku ne cewa a ’yan kwananin nan an yi rikice-rikice tsakanin gungu-gungun matasa, wasunsu dauke da makamai iri-iri.

“To gwamnati ba za ta lamunci wannan ba, kuma ta haramta dabanci.”

– Babu gudu, babu ja da baya –

Ya ce, “Na san mutane suna nan suna ta ce-ce-ku-ce game da matakin da aka dauka, amma ina tabbatar muku cewa babu gudu, babu ja da baya a wannan mataki da Gwamna Zulum ya dauka.”

Kwamishinan ya ce daga cikin shugabannin kungiyoyin matasa 186 da suka halarci zaman da gwamnan ya kira, wasunsu ba masu tayar da zaune tsaye ba ne, amma “akwai wasu masu kunnen kashi.”

A cewarsa, Gwamna Zulum ba zai daina biyan alawus ga matasan jihar marasa aikin yi ba da ya fara shekara biyu da suka gabata.

“Bayan haka ya ba da umarnin a dauki karin matasa 1,000 a koya musu sana’ar kanikanci da aikin kafinta sannan a ba su abin da za su dogara da kansu,” inji shi.

Kwamishinan ya ce ma’aikatarsa za ta hada kai da Ma’aikatar Kimiyya da Kere-kere domin horas da karin matasa 1,500.

Sannan ya yi kira ga iyaye da su rika kula da ’ya’yansu, yana mai jaddada cewa dokar hana bara a kan tituna tana nan tana aiki.