✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A karon farko cikin shekara 397 duniyoyin Jupiter da Saturn za su hadu

Wannan dai shine karo na farko da duniyoyin biyu za su zo kusa da juna tun shekarar 1623.

A daren ranar Litinin, 21 ga Disamba, 2020, duniyoyin Jupiter da Saturn za su hadu a karon farko tun shekarar 1632 rabon da hakan ya faru.

Duniyoyin biyu zau su dab da juna ne a karo na farko tun bayan da suka taba yin haka a karni na 17, shekara 397 da suka gabata.

“Abin da ba kasafai ake samu ba shi ne duniyoyin su hadu a kusa da juna da daddare,” inji Farfesa David Weintraub, masani a kan ilimin sararin samaniya a Jami’ar Vanderbilt.

Masana Ilimin Sararin Samaniya sun ce ba kasafai akan samu haduwar manyan duniyoyin biyu a falaki daya ba, saboda Jupiter takan wuce makwabciyarta ta Saturn a kan falakai daban-daban kusa da rana duk bayan shekaru 20.

Idan yanayi ya bari, za a iya ganin su jim kadan da faduwar rana a kuryar Kudu maso Yamma.

Saturn dai za ta kasance mafi kankanta kuma za ta fito dishi-dishi daga saman Jupiter.

Sai dai duk da bayyanar tasu da za a samu, za su kasance ne da nisan kilomita miliyan 730 daga doron kasa, yayin da Jupiter kuma za ta kasance tana da nisan kilomita 890 daga doron kasa.

“Za mu iya cewa a kan samu faruwar haka kamar sau daya a tsawon rayuwar kowanne mutum.

“Ina ganin duk abin da za a iya samu sau daya a tsawon rayuwa za a iya cewa ba kasafai yake faruwa ba”, inji masanin.

Wannan dai shi ne karo na farko da duniyoyin biyu za su zo kusa da juna tun shekarar 1623.

Sai dai masana sun ce zai yi wuya a iya ganin haduwar tasu saboda kusancin duniyoyin biyu da rana.

Rabon da su zo dab da juna kamar haka tun a watan Maris na shekarar 1226, kuma ba za su sake haduwa kamar haka ba sai nan da 15 ga watan Maris na 2080.