✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A rika yi wa gwamnatina adalci kan matsalar tsaro —Buhari

Mun yi iya bakin kokarinmu kuma za mu ci gaba da yi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan Najeriya da su rika yi wa gwamnatinsa adalci a duk lokacin da suke sharhi kan batun matsalar tsaro.

Buhari ya bukaci ’yan Najeriya da suka rika kwatanta hobbasan da gwamnatinsa ta yi wajen magance matsalar tsaro idan an yi la’akari da abin da ta gada tun a 2015.

Wannan furuci na Buhari na zuwa ne a lokacin da Khalifan Tijjaniyya na duniya ya kai masa ziyara a ranar Juma’a, inda shugaban ya bayyana cewa ya kamata jama’a su rika magana kan irin nasarorin da suka samu a bangaren tsaro musamman a Arewa maso Gabas da kuma Kudu maso Kudancin kasar.

Manyan bakin da suka ziyarci Buhari
Bangaren Gwamnatin Tarayya da suka tarbi bakin

Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa na sane da irin hakkokin da suka rataya a wuyanta da suka shafi tsaro inda ya ce za su ci gaba da yin iya bakin kokarinsu.

Shugaban ya kuma bukaci ’yan Najeriya da su bayar da hadin kai da kuma nuna goyon baya a harkar tsaro da kuma yaba wa ayyukan da gwamnati ke yi.

A cewarsa, “mun yi iya bakin kokarinmu kuma za mu ci gaba da yi ta hanyar samar da tsare-tsare masu kyau domin yaki da ta’addanci. Ina fata Allah zai karbi addu’ar mu.”

Daga cikin tawagar da ta ziyarci shugaban kasar har da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Sheikh Dahiru Usman Bauchi.