✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abdullahi Adamu ya yi murabus daga Majalisar Dattawa

Sabon Shugaban APC na Kasa ya yi murabus daga kujerarsa ta dan Majalisar Dattawa.

Sabon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ajiye kujerarsa ta dan Majalisar Dattawa.

A safiyar Talata ne Sanata Abdullahi Adamu ya sanar da Majalisar cewa ya sauka daga kujerar dan Majalisar Dattawa Mai Wakilatar Nasarawa ta Yamma.

Hakan na kunshe ne a takardar ajiye aiki da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, mako biyu da zamansa shugaban jam’iyyar APC mai mulki.

A zaman Majalisar ta ranar Talata shi ma Mataimakin Shugaban Jam’iyar APC na Kasa Mai Wakiltar Yankin Arewa, Sanata Abubakar Kyari ya mika takardarsa ta sauka daga kujerar dan majalisa mai wakiltar Borno ta Arewa.

Kafin saukarsu daga majalisar, Sanata Abubakar Kyari shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Birnin Tarayya; Abdullahi Adamu shi ne Shugaban Kwamitin Ayyukan Gona da Raya Karkara.

’Yan majalisar su biyu, sun yi murabus ne bayan darewarsu kan kujerar shugabancin Jam’iyyar APC mai mulki, a babban taron jam’iyyar da ya gudana ranar 26 ga watan Maris.

Tun bayan darewar tasu a bisa kujerar jagorancin jam’iyyarsu ake ta ce-ce-ku-ce game da halascin ci gaban da zamansu a matsayin ’yan majalisa da kuma shugabannin jam’iyya.

A kan haka ne dai wasu ke ta ce sai dai su hakura da kujerunsu ta Majalisar Datttawa.

Yanzu dai Borno ta Arewa, wadda Sanata Abubakar Kyari ya wakilta da Nasarawa ta Yamma, wadda Abdullahi Adamu za su kasance ba su da wakilai a Majalisar Dattawa.

Abin da ya rage gaba, shi ne majalisa ta sanar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) game da gibin da aka samu a wadannan mazabu.

Yin hakan a hukumace, shi ne zai ba wa INEC damar shirya gudanar da zaben cike gurbi a mazabun a nan gaba.