Abdulsalami da Sarkin Musulmi za su jagoranci taron Daily Trust karo na 19 | Aminiya

Abdulsalami da Sarkin Musulmi za su jagoranci taron Daily Trust karo na 19

Abdulsalami Abubakar
Abdulsalami Abubakar
    Sagir Kano Saleh

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ada Abubakar da tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami Abubakar za su jagoranci Babban Taron Tattaunawa na Shekara-shekara na Daily Trust na 2022.

Taron wanda shi ne karo na 19, zai gudana ne da misalin karfe 10 na safe, a ranar Alhamis, 20 ga watan Janairun 2022 a Abuja, inda Abdulsalami zai jagoranci taron, Sarkin Musulmi kuma zai kasance Uban Taro.

Kamfanin Media Trust masu buga jaridar Daily Trust, Aminiya da sauran dangoginsu, shi ne yake shirya taron, wanda takensa a wannan karon shi ne ‘2023: Siyasa, Tattalin Arziki da kuma Rashin Tsaro’.

Dokta Murtala Ahmed Rufa’i daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato, wanda kuma ya gudanar da wani zuzzurfan bincike kan ayyukan ’yan bindiga mai suna ‘Ni Dan Bindiga Ne’, wanda ya dauki hankali matuka, tare da kwararren masanin harkar tsaro, Dokta Kabir Adamu na kamfanin nazari kan tsaro na Beacon Consulting Limited da ke Abuja, su ne za su tattauna a kan maudu’in.

Taron zai gudana a Cibiyar Taro ta Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ke hanyar unguwar Gwarimpa, daura da Babban Shagon Kasuwanci na NEXT a Rukunin Gidaje na Kado da ke Abuja.

Babbar Mai Jawabi ita ce Misis Ifueko Omoigui Okauru, tsohuwar Shugabar Hukumar Karbar Haraji ta Kasa (FIRS), sa’annan kwararriya kuma shaharariyar ’yar jarida kuma shugabar Kamfanin Sadarwa na Dariya, Kadaria Ahmed, ita ce za ta gabatar da tattaunawar.

Manyan baki a wurin taron sun hada da gwamnoni da tsoffin gwamnomi da sauran manyan mutane.

Za a yada taron kai-tsaye ta shafukan sada zumunta na Facebook da Instgaram na Daily Trust da kuma Trust TV. Aminiya za ta kawo muku hotuna da sauran abubuwa daga wurin.

Ana bukatar mahalarta su kasance sanye da takunkumi da tare da kiyaye dokokin kariyar COVID-19.