✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da malaman Kano suka faɗa kan ajiye aikin Daurawa

Sheikh Rijiyar Lemo ya ce ana nema a maida Kano dandalin baɗala, dandalin fasiƙanci da fajirci!

Malaman Addinin Musulunci a Kano sun magantu kan murabus ɗin da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi daga mukaminsa na Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa, a safiyar ranar Juma’a ce babban malamin ya sanar da sauka daga mukamin a cikin wani saƙo na bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Sheikh Daurawa ya ɗauki matakin ne kwana guda bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya soki Hukumar Hisbah bisa salon ayyukanta waɗanda ya ce suna keta doka.

Sheikh Daurawa ya ce gwiwoyinsa sun yi sanyi bayan da ya saurari kalaman gwamnan kan sukar da ya yi wa Hukumar Hisbah.

Sai dai a jawabin Sheikh Daurawa, ya bai wa gwamnan haƙuri sannan ya bayyana cewa ya sauka daga muƙaminsa.

“Mun yi iya kokarinmu, mu ga cewa muna abin da ya kamata, to amma ina ba mai girma gwamna hakuri bisa fushi da ya yi da maganganun da ya faɗa.

“Kuma ina rokon da ya yi min afuwa, na sauka daga wannan mukami da ya ba ni na Hisbah, inda muka yi kuskure muna fata a yafe mana. Kuma ina yi masa masa addu’a da fatan alheri.”

Sai dai kuma a wasu bidiyoyi da suka karade soshiyal midiya, malaman da suka haɗa da Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya da Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo, sun bayyana rashin jin daɗinsu da kuma yadda suke ganin za a tari hanzarin lamarin.

A  bidiyon farko da Dokta Gadon Ƙaya ya fitar, ya yaba wa Gwamnan Kano kan ayyukan alherin da yake kawowa jihar, da kuma ƙoƙarinsa na karbar gyara daga al’ummarsa.

Sai dai ya ce akwai buƙatar Gwamnan ya tausasa zuciyarsa ya zauna da Malam Daurawa, domin tattaunawa da shi ya kuma ba shi haƙuri.

“Muna kira ga gwamna Abba Yusuf da waɗanɗa ke kusa da shi su kai zuciya nesa su kira Malam Daurawa, su zauna da shi kuma su ba shi haƙuri kan abubuwan da suka faru.”

A cikin bidiyon, Sheikh Abdallah Gadon Ƙaya ya ce ya kamata Gwamna Abba Yusuf ya duba al’ummar Jihar Kano da ci gaban da Malam Daurawa ya kawo, baya ga gudummawar da yake bai wa ita kanta gwamnatin ta Kano.

“Ya kamata a zauna da shi Malam Daurawa a ba shi shawarwari a kan abubuwan ya yake yi ko ake ta cewa Hisbah take yi,” in ji Gadon Ƙaya.

“Matsayin Malam Daurawa ya kai kuma darajarsa ta kai.”

Kazalika, Gadon Ƙaya ya kuma bai wa Sheikh Daurawa haƙuri, da kuma roƙon ya amsa kiran Gwamna idan har ya buƙaci hakan, domin ci gaban jihar da kuma kukan da al’ummar jihar ke yi saboda ajiye aikinsa.

A nasa bangaren, Dokta Sani Umar Rijiyar Lemo kokawa ya yi da yadda Kano ta zama cibiyar yaɗa baɗala ta dandalin sada zumunta, da kuma yadda manyan jihar suka zuba ido ba tare da ɗaukar mataki ba.

Ya bayyana cewa, “ana nema a maida Kano dandalin baɗala, dandalin fasiƙanci da fajirci! Ana tasowa daga garuruwa masu nisa a zo cikinta domin a yi baɗala.

“Ba ma garuruwa ba, har ta kai yanzu daga ƙasashe maƙota ake ƙetarowa, yarinya ta baro iyayenta, ta shigo jihar, ta kama ɗaki da gida ta fara yaɗa baɗala.

“Tiktok ɗin nan yana yi a ko’ina in dai akwai network, amma ba su yarda su yi a ƙasarsu ba, ba su yarda su yi a cikin ’yan uwansu ba, saboda suna jin kunyar ’yan uwansu ko kuma ba za su ƙyale su ba, amma za su iya takowa su zo Kano su kama gida, su riƙa yin taswirar kanta cikin ƙazantacciyar shiga, da kalamai na batsa marasa kyau, suna antayo wa ’ya’yanmu.

“Ana ji ana gani ana sane da masu yin wannan abu amma an zuba musu ido. To idan ba a tashi tsaye ba aka taka musu burki aka yi abin da ya dace ba, babu shakka idan Allah Ya tashi kama mu da azaba, ba su kaɗai zai yi wa ba. Laifinmu shi ne ba mu yi wani abu ba,” inji shi.

Haka zalika, Sheikh Rijiyar Lemo ya jaddada cewa ƙoƙarin da Hisbah ke yi na umarni da kyakkyawa da yaƙi da baɗalar ne ɗaya daga cikin abubuwan da suka sanya ake samun sauƙi a jihar.

“Jiha ce da ta kowacce fuska za a cuta idan ɓarna ta shigo saboda yawan al’umma da dukiyar da ke ciki, amma Allah Ya tsare ta.”

Ya kuma ja hankalin gwamnati, da shugabanni, da sarakuna, haɗi da sauran malaman jihar kan illar zuba ido hakan ta ci gaba da faruwa, domin a cewarsa azabar da za ta game kowa ce a ƙarshe za ta faɗowa al’umma.