✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka rufe dukkan matatun mai —NNPC

Matatun sa aiki yadda ya kamata, ana kashe kudi a kansu amma kuma asara ake yi

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) Mele Kolo Kyari ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ta rufe dukkannin matatun mai da ke Fatakwal, Warri da Kaduna ne saboda ba sa aiki yadda ya kamata.

Kyari ya bayyana hakan ne a cikin wani shiri mai suna Politics Today na gidan talbijin na Channels ranar Laraba.

Shugaban kamfanin ya ce, “Da farko dai mun rufe dukkan matatun mai guda hudu ne da ke birane uku saboda dalilai guda biyu.

“Ayyukan barayin mai masu fasa bututan mai na daya daga cikin manyan kalubalen da muke fuskanta kuma ya hana mu aiki.

“Hakan dai na nufin ba za mu iya tura man zuwa matatun ba yadda ya kamata.

“Na biyu kuma akwai bambanci tsakanin yin kwaskwarima da kuma gyaran matatu. Kwarya-kwaryar gyara shi ne abinda kowacce matata ke yi ba wai garanbawul ba.

“A ka’ida kamata ya yi kowace matata na yin aikin da ya kai kamar kaso 90 cikin dari na karfinta. Amma duk da gyare-gyaren da muka yi da duk wani hobbasa da muka yi mun gaza cimma hakan shi ya sa muka dauki matakin rufe su.

“Kiyasin da muka yi shi ne za su yi aikin da ya kai kaso 60 cikin 100, amma sai muka fahimci yin hakan kamar zai zama illa.

“Za ka dauki mai na Dala 100 zuwa matata amma daga karshe ka sami Dala 70, hakan ina ganin babu wata fa’ida a ciki”, inji shugaban kamfanin.

Gwamnati mai ci dai ta yi alkawarin gyara dukkan matatun man da ke Najeriya a lokacin yakin neman zabe tare da tabbatar da cewa Najeriya ta daina shigo da tataccen mai daga kasashen ketare.

Sai dai duk irin yunkurin da aka yi da makudan kudaden da aka narka wajen gyaran matatun, da alama har yanzu hakar gwamnatin ta gaza cimma ruwa.