✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na yi imanin zan ci zabe a 2023 —Tinubu

Mu sani cewa duk abin da ya faru a wata jiha daya to ya shafi kasar ce baki daya.

Babban jagora a jam’iyyar APC mai mulkin kasar, Asiwaju Bola Tinubu, ya sake bugun gaba tare da bayyana kwarin gwiwar cewa shi zai lashe zaben shugaban kasa a badi.

Tinubu dai na daya daga cikin manema takarar kujerar shugaban kasa a zaben na badi da suka bayyana ra’ayinsu karara a bainar jama’a.

A yayin ziyarar da ya kai wa Sanata Rashidi Ladoja, tsohon gwamnan Jihar Oyo a gidansa da ke babban birni na Ibadan a karshen mako, Tinubu ya ce matukar talakawa kasar nan za su fito kwansu da kwarkwata su kada kuri’a, babu abin da zai hana shi cin zabe.

Sai dai kamar yadda masu iya magana kan ce a rika sara ana duban bakin gatari, Tinubu ya kuma bayyana cewa tabbas akwai babban kalubale amma yana fatan hakarsa za ta cimma ruwa.

A makon da ya gabata ne jagoran na jam’iyyar APC ya sanar cewa babu abin da zai hana mai nadin sarkin zama sarki, la’akari da cewa yanna daya daga cikin jiga-jigan da suka tsaya tsayin-daka wajen ganin Buhari ya samu nasara a zaben 2015, lamarin da ya sanya yake bugun gaba zai gaji kujerarsa a zaben 2023.

Wannan dai na zuwa ne a bayan ya sanar da Shugaba Muhammadu Buhari kudirinsa na neman takarar kujerar shugaban kasa a babban zaben na 2023 da ke tafe.

Da yawa daga cikin manema takarar kujerar shugaban kasar a jam’iyyar PDP da APC sun bayyana ra’ayin neman takara tun bayan da Tinubu ya bayyana nasa a makon ya gabata.

Tinubu ya fara shawagi a Arewa

Duk da dai lokacin da aka sahalewa manema takara fara yakin neman zabe na nan tafe, bayanai sun ce Tinubu ya fara karade wasu jihohin Arewa, inda a kwanan nan ya kai ziyara Jihar Zamfara domin jajanta wa al’umma a kan hare-haren ’yan daban daji da ke kara ta’azzara, yana mai cewa saura kiris lamarin ta’addanci ya zama tarihi.

Aminiya ta ruwaito cewa, Tinubu ya bayar da gudunmuwar naira miliyan 50 a matsayin tallafi ga al’ummar Kananan Hukumomin Bukkuyum da Anka wadanda harin ’yan bindiga ya yi musu sanadiyyar rayukan akalla mutum 58 a makon jiya.

Bayan Zamfara ya kai ziyara Katsina

Tinubu ya kuma kai ziyara Jihar Katsina, inda ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar dangane da rasuwar Dokta Rabe Nasir, Kwamishinan Gwamna Aminu Bello Masari da aka kashe a bara.

A Jihar Katsina, Tinubu ya tunatar da al’umma cewa kasancewar Katsina na daya daga cikin jihohin da matsalar tsaro ta yi kamari, amma su sani cewa duk abin da ya faru a wata jiha to ya shafi kasar ce baki daya.