✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa Najeriya ba za ta daina cin bashi ba – CBN

A cewar Emefiele, babu wani laifi a ciyo bashi matukar za a yi amfani da shi domin kyakkyawar manufa.

Babban Bankin Kasa na CBN ya ce Najeriya ba za ta daina ciyo bashi ba matukar bukatar yin hakan ta taso don biyan bukatun ’yan kasarta.

Gwamnan bankin, Mista Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a, yayin wata tattaunawa a kan yadda basussukan kasar ke dada hauhawa a kullum.

Kungiyar ActionAid Nigeria (AAN) ce dai ta shirya taron mai taken, “Hauhawar basussukan Najeriya da kuma kalubale da ci gaba” domin lalubo bakin zaren matsalar, musamman yadda ta ce basukan da kuma talauci sun karu matuka a mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A cewar Emefiele, wanda Mataimakin Darakta Sashen Tsara Manufofin ba Bankin, Dakta Tawose Joseph ya wakilta, babu wani laifi a ciyo bashi matukar za a yi amfani da shi domin kyakkyawar manufa.

Ya ce, “Bashi na daga cikin harkokin kudi, kuma ciyo shi ba zai taba zama laifi ba. Kamfanoni masu zaman kansu na aro kudi domin su ci gaba da harkokinsu.

“Amma abin da ya fi muhimmanci shine yin amfani da kudaden bashin yadda ya kamata. Ana cin bashi ne in aka sami gibi a kudaden shiga.

“Idan ka kwatanta abinda ake samu da wanda ake kashewa za ka fahimci cewa babu wata matsala. A inda barazanar take shine idan cin bashin ya wuce gona da iri.

“CBN ya fahimci cewa idan tattalin arzikinmu na cikin tsaka mai wuya sannan ba a ciyo bashi ba to za mu fada cikin gagarumar matsala. Hakan ne ya sa muka fito da managartan hanyoyin takaita hauhawar farashin kayayyaki,” inji Gwamnan Babban Bankin.

Ya kara da cewa CBN ya kuma fito da hanyoyin da za su taimakawa masu karamin karfi, lamarin da ya ce ya yi matukar tasiri.

Gwamnan ya kuma ce bankin ya bullo da shirye-shirye har iri 37 domin bunkasa tattalin arziki, ko da yake ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba.