✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubakar Tsav ya riga mu gidan gaskiya

Allah ya yi wa fitaccen mai sharhi a kan al’amuran tsaro, kuma tsohon kwamihsinnan ’yan sanda, Alhaji Abubakar Tsav rasuwa. Wani na hannun damansa ne…

Allah ya yi wa fitaccen mai sharhi a kan al’amuran tsaro, kuma tsohon kwamihsinnan ’yan sanda, Alhaji Abubakar Tsav rasuwa.

Wani na hannun damansa ne ya tabbatar wa manema labarai rasuwar a Makurdi, babban birnin jihar binuwai.

Torkuma Uke ya ce Alhaji Abubakar ya rasu ne a Babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke birnin na Makurdi ranar Litinin, bayan wata gajeriyar jinya.

Marigayin ya taba zama kwamishinan yan sanda a jihar Legas, sannan kuma ya rike mukamin kwamishina mai wakiltar jihar Binuwai a Hukumar Sauraren Koke-koken jama’a ta kasa.

Alhaji Abubakar Tsav sanannen mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, musamman al’amuran da suka shafi tsaro, wanda ba ya shakkar tsage gaskiya.