✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘ADP za ta tika APC da PDP da kasa a zaben badi a Kano’

ADP tana da manufofi da kuma tsare-tsare na ci gaban matasa da kuma tafiya da zamani.

Jam’iyyar ADP ta ce za ta tika jam’iyyar APC da ta PDP a kasa a Zaben Gwamnan Jihar Kano da za a yi a badi.

Wannan dai furucin wani tsohon Kwamishina ne kuma tsohon Sakataren APC da kuma ANPP na Jihar Kano, Alhaji Rabiu Bako.

 

Rabiu Bako ya yi wannan ikirari ne a hirar sa wani gidan radiyo a jihar Kano, wanda kuma Aminiya ta saurara karshen mako.

Tsohon kwamishinan ya ce, duk da cewa jam’iyyar ADP sabuwa ce a Jihar Kano, amma tasirinta da tsarinta ya kai da cewa za ta yi gogayya da wadannan tsaffin jam’iyyu, har su sha kaye a hannunta a zabe mai zuwa.

Rabiu Bako ya lissafo rikicin cikin gida, da rashin tsari da kuma alkibla a yanzu a matsayin wasu daga cikin abubuwan da za su kayar da jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa a jihar.

Haka kuma ya ce, abin da zai sa jam’iyyar APC mai mulki ta sha kasa a zaben shi ne, salon mulkin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ce ya zo da rashin adalci da rashin mutunta masu mutunci a jihar, da kuma karyar ilimi kyauta da ta yi.

“Duk duniya ko da ana yaki ne babu inda ake taba kudin ‘yan fansho domin hakkinsu ne tun da sun bauta wa gwamnati, amma ban da jihar Kano, wanda a yanzu Gwamnatin Jihar ta zuba kudadensu a aljihunta,” in ji Rabiu Bako.

Tsohon Sakataren APC ya ce, NNPP ce kawai za ta iya kafada da kafada da ADP a Kano, kuma ko ita sai sun kayar da ita a zabe, saboda manufofi da kuma tsare-tsaren da dan takararta, Sha’aban Sharada ya zo da su na ci gaban matasa da kuma tafiya da zamani.

Alhaji Rabiu Bako shi ne shugaban jam’iyyar ADP kuma abokin takarar Sha’aban Sharada a takarar kujerar gwamnan Kano a jam’iyyar.