✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Afghanistan: Mayakan Taliban da sojoji 9 sun kwanta dama

Mayakan kungiyar Taliban takwas da soja daya sun mutu bayan ga wasu tara da suka samu raunuka a harin da kungiyar ta kai yankin Darqad…

Mayakan kungiyar Taliban takwas da soja daya sun mutu bayan ga wasu tara da suka samu raunuka a harin da kungiyar ta kai yankin Darqad na Arewacin Lardin Takhar na kasar Afghanistan.

Kakakin Lardin Takhar, Abdul Khalil Asir ya ce sojojin gwamnatin kasar sun tarwatsa mayakan na Taliban a harin na ranar Asabar, wanda ya bar sojoji biyar da mayakan kungiyar da raunuka.

“Mayakan Taliban sun kaddamar da wani babban hari da nufin kwace Hedikwatar yankin Darqad da misalin karfe 01:00 na safiyar yau (Asabar).

“Dakarun gwamnati sun mayar da martani suka tarwatsa maharan da suka cika bujensu da isa bayan an jikkata su,” kamar yadda Abdul ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na Xinhua.

Duk da cewa bai yi cikakken bayanin abin da ya faru ba, wani hafsan soji, Abdul Razeq, ya ce “an kashe mayakan Taliban takwas da soja daya, an kuma jikkkata wasu mutum tara, da suka hada da sojoji biyar, a musayar wutar da aka yi awa biyu ana gwabzawa.”

Mayakan Taliban sun sha yi kokarin neman kwace ikon yankin Darqad ba tare da samun nasara ba a tsawon shekaru.